Da dumi-dumi: Umahi ya yi murabus a matsayin shugaban kwamitin tsaro na Kudu maso Gabas

Da dumi-dumi: Umahi ya yi murabus a matsayin shugaban kwamitin tsaro na Kudu maso Gabas

- Kungiyar tsaro ta gabas, Ebubeagu, na iya haduwa da cikas yayin da shugabanta na farko, Manjo Janar Obi Umahi (mai ritaya), ya yi murabus

- Umahi ya bayyana murabus din nasa ne a ranar Litinin, 7 ga watan Yuni, a wata wasika da ya aike wa shugaban kungiyar Ohanaeze Ndigbo, Ambasada George Obiozor

- A cewarsa, Umahi ya ce tun da aka kafa kungiyar tsaron, gwamnonin kudu maso gabas sun hana ta kudi

Manjo Janar Obi Umahi (mai ritaya), shugaban Ebubeagu, kwamitin tsaro na kudu maso gabas, ya yi murabus daga mukamin.

Jaridar PM News ta bada rahoton cewa kungiyar gwamnonin kudu maso gabas a ranar 31 ga watan Agusta, 2019, ta nada Janar Umahi a matsayin shugaban kwamitin.

KU KARANTA KUMA: Bidiyo ya nuno shugaban kasar Amurka mai shekaru 78 da matarsa suna tuka kekuna a kan titi, an yi cece kuce

Da dumi-dumi: Umahi ya yi murabus a matsayin shugaban kwamitin tsaro na Kudu maso Gabas
Da dumi-dumi: Umahi ya yi murabus a matsayin shugaban kwamitin tsaro na Kudu maso Gabas Hoto: David Umahi
Asali: Facebook

Ebubeagu ba shi da kudi, kayan aikin magance matsalar rashin tsaro

Legit.ng ta tattaro cewa Umahi ya yi murabus ne a ranar 4 ga watan Yuni, a wata wasika da ya aike wa shugaban kungiyar gwamnonin, yana korafin rashin kudi da ofis.

Jaridar Punch ta kuma ruwaito cewa an aika wasikar zuwa ga shugaban kungiyar Ohanaeze Ndigbo, Ambasada George Obiozor.

Wasikar ta ce:

“Tunda aka kafa wannan kwamiti na tsaro, mun yi shawarwari kuma muka amince kan hanyoyin da za a bi don wayar da kan mutane har zuwa matakin al’umma a yankin Ibo, yanayin yadda ake gudanar da su, kayan aiki da wasu nau’ikan kayan aikin da ake bukata, kamar su jirage marasa matuka, motoci da sauransu Mun kuma kirkiro batun tsaron SE."
“Cikin girmamawa ina neman cewa Mai martaba ya ba ni izini na sauka daga mukamina na shugaban Kwamitin Tsaro na Kudu maso gabas. Dangane da kaunar da nake yi wa Ndigbo, ina baku tabbacin cewa koyaushe zan kasance a shirye don ba da shawara kan nasarar Ebube Agu ba tare da cikas ba."

Gwamnonin kudu maso gabas a ranar 11 ga Afrilu, sun sanar da kafa EBUBEAGU a Owerri, inda suka kara da cewa mambobin kwamitin tsaro da manyan lauyoyin jihohin kudu maso gabas su biyar sun sake duba tsarin dokar da ta dace da tsaro na Ebubeagu.

KU KARANTA KUMA: 2023: Atiku ya mayar da martani game da kudirinsa na shugabancin kasa, ya magantu kan fastocinsa da Soludo

A wani labarin, mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar na III, ya ce wasu tsirarun manyan mutane a Nigeria da ke tunanin dole sune za su rika juya kasar suna kokarin tarwatsa kasar, Daily Trust ta ruwaito.

The Nation ta ruwaito cewa Sultan din wanda ya yi wannan furucin a ranar Litinin a Bauchi yayin kaddamar da sansanin maniyatta aikin hajji ya ce akwai bukatar daukan matakin gaggawa domin karfafa gwiwar yan Nigeria domin akwai 'shedanu' da yawa a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel