Ba Fasto ba, ko kai waye idan ka hau Twitter ka jira hukunci, Lai Mohammed

Ba Fasto ba, ko kai waye idan ka hau Twitter ka jira hukunci, Lai Mohammed

- Ministan yada labarai a Najeriya ya sake jaddada hukuncin gwamnatin na dakatar da Twitter

- Ministan ya ce lallai duk wanda ya taka dokar to lallai ya jira ranar da za a gurfanar dashi kawai

- Sai dai, ya bayyana cewa, akwai wadanda za a gurfanar akwai kuma wadanda ba za a gurfanar ba

Lai Mohammed, Ministan yada labarai na Najeriya, ya bayyana karara cewa ‘yan Najeriya da suka shiga shafin Twitter, ciki har da Fasto Enoch Adeboye, ya kamata su jira gurfanarwa.

Lai Mohammed ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da BBC Africa Focus a ranar Litinin lokacin da aka tambaye shi ko za a gurfanar da Mista Adeboye saboda amfani da Twitter.

Lai Mohammed ya ce: "To Babban Lauya ya bayyana a fili cewa idan wani ya karya doka, za a hukunta wannan mutumin."

KU KARANTA: Zan karfafa muku cin naman Alade a madadin na Shanu, Akeredolu ga 'yan jiharsa

Ba Fasto ba, ko kai waye idan ka hau Twitter ka jira hukunci, Lai Mohammed
Ba Fasto ba, ko kai waye idan ka hau Twitter ka jira hukunci, Lai Mohammed Hoto: dw.com
Asali: UGC

Ministan wanda ya bayyana haka a rude ya kuma shaida cewa za a gurfanar da wasu 'yan Najeriya yayin da wasu kuma ba za a gurfanar da su ba.

Ya ce ofishin Babban Lauyan shi "zai yanke hukunci kan wanda ya kamata a gurfanar da kuma wanda ba za a gurfanar ba."

PM News ta ruwaito cewa, Fasto Adeboye ya yi amfani da shafinsa na Twitter ranar Litinin da kuma na RGGC.

Babban malamin da ake girmamawa ya kuma ba da hujja da nacewarsa ta amfani da dandalin tare da ishara ga Mataki na 19 na Majalisar Dinkin Duniya game da Hakkokin Dan-Adam (UDHR).

Hakazalika, babban mai kula da cocin Deeper Life Bible Church, Williams Kumuyi, ya ce sakonnin da Adeboye ya aike ya tura su ne ga duniya, nahiyoyi biyar kuma sama da kasashe 100.

Sai dai, Lai Mohammed ya jaddada a cikin hirar cewa ci gaba da amfani da Twitter a Najeriya yana nuna raina kasancewar kasar mai cikakken iko.

“Gwamnati ta dakatar da ayyukan Twitter a Najeriya har abada, saboda ci gaba da amfani da dandalin don ayyukan da za su iya lalata kasancewar Najeriya mai cikakken iko da gwamnati.

"Har ila yau, an umurci Hukumar Watsa Labarai ta Kasa da ta hanzarta fara aiwatar da lasisin duk ayyukan kafofin watsa labarai a Najeriya," in ji shi.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun yi kaca-kaca da masarauta, sun kone gidaje sama da 60

A wani labarin, Biyo bayan umarnin gwamnatin tarayya na dakatar ayyukan Twitter a Najeriya, an samu wasu gwamnonin Najeriya da suka yi kunnen kashi suka yi rubutu a shafin na Twitter.

Gwamnonin jihohin Kaduna da Ondo, Nasir El-Rufai da Rotimi Akeredolu, suka bijirewa wannan umarni na gwamnati, Premium Times ta ruwaito.

Dukkanin gwamnonin, wadanda suke mambobin jam’iyyar APC mai mulki, sun yi rubutun a Twitter, ba tare da tsoron barazanar Babban Lauyan Tarayya da Ministan Shari’a, Abubakar Malami na hukunta masu yin Twitter ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel