Gwamnonin kudu yan wasan barkwanci ne – Kungiyar Miyetti Allah

Gwamnonin kudu yan wasan barkwanci ne – Kungiyar Miyetti Allah

- Kungiyar makiyaya ta kasa, Miyetti Allah ta kalubalanci matsayar gwamnonin kudu dangane da kudirin dokar hana kiwo a fili a yankin

- A cewar shugaban kungiyar na kasa, Alhaji Bello Bodejo, dukka gwamnonin jihohin kudu 17 yan wasan barkwanci ne

- Ya ce babu kundin tsarin mulki da ya basu karfin aikata abunda suka yi

Kungiyar al'adu ta Fulani, Miyetti Allah, ta bayyana gwamnoni 17 na Jihohin kudu a matsayin yan wasan barkwanci.

Shugaban kungiyar na kasa, Alhaji Bello Bodejo, ne ya bayyana hakan a cikin wata tattaunawa da ya yi da jaridar Daily Sun, a garin Abuja, dangane da kudirin dokar hana kiwo a fili a yankin, inda ya ce bai rataya wuyan mambobinsa ba.

KU KARANTA KUMA: 2023: Atiku ya mayar da martani game da kudirinsa na shugabancin kasa, ya magantu kan fastocinsa da Soludo

Gwamnonin kudu yan wasan barkwanci ne – Kungiyar Miyetti Allah
Gwamnonin kudu yan wasan barkwanci ne – Kungiyar Miyetti Allah Hoto: Nigerian Governors' Forum.
Asali: Facebook
“Gwamnoni ba su da iko na kundin tsarin mulki don aikata abin da suka yi. Kodayake, suna da 'yancin yin sanarwa ko shawarwari, amma bai rataya a wuyanmu ba saboda babu goyon bayan tsarin mulki ga hakan. Dukkansu 'yan wasa ne.”

Ya shawarci al’umman Fulani da ke kudu da su ci gaba da zama a can kuma su yi kasuwancinsu bisa doka, saboda su ‘yan Najeriya ne kuma ya kamata a ba su damar yin kasuwanci cikin lumana a ko’ina a cikin kasar.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Umahi ya yi murabus a matsayin shugaban kwamitin tsaro na Kudu maso Gabas

Ya kalubalanci gwamnonin da su bi mutanen da ke aikata laifuka a cikin garuruwan kudu ba tare da la'akari da ƙabila ko addini ba.

A halin yanzu, kungiyar Miyetti Allah ta nisanta kanta daga hare-haren ranar Lahadi a Igangan da ke karamar hukumar Ibarapa ta Arewa a jihar Oyo, Shafin LindaIkeji ya ruwaito.

Ta kalubalanci 'yan sanda da sauran jami'an tsaro da su hanzarta gudanar da bincike, kame da kuma hukunta mutanen da aka samu da hannu a hare-haren don yin karen tsaye ga wasu da ke son aikata irin wannan laifin.

Ya ce mambobin kungiyar mutane ne masu son zaman lafiya, wadanda ba za su iya shiga cikin irin wannan mummunan aikin ba.

Don haka, ya yi kira ga Fulanin da ke fadin kasar nan da su kwantar da hankulansu, su kasance masu son zaman lafiya da bin doka da oda duk da yawan tunzura.

A bar yan kabilar igbo idan ballewa suke so, ba za mu iya wani yaki ba: Dattawan Arewa

A gefe guda, Kungiyoyin 'yan asalin yankin Biafra (IPOB) da kungiyar fafutukar tabbatar da kasar Biyafara mai mulkin mallaka (MASSOB) suna yakin neman rabewar yankin kudu maso gabas daga Najeriya.

Nnamdi Kanu ne ya kirkiri kungiyar IPOB a shekarar 2012, yayin da RSh Ralph Uwazuruike ya kafa kungiyar MASSOB a shekarar 1999.

Da yake zantawa da manema labarai bayan wata ganawar sirri da aka yi a Abuja a ranar Litinin, Hakeem Baba-Ahmed, mai magana da yawun kungiyar, ya ce hargitsin da Ibo ke yi na ballewa ya fara yin yawa, yakara da cewa shugabannin kasar sun nuna goyon bayan wannan shawarar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel