Tashin Hankali: An Tsinci Gawar Ɗaya Daga Cikin Ɗaliban Islamiyya da Yan Bindiga Suka Sace a Neja

Tashin Hankali: An Tsinci Gawar Ɗaya Daga Cikin Ɗaliban Islamiyya da Yan Bindiga Suka Sace a Neja

- An gano gawar ɗaya daga cikin ɗaliban da aka sace a islamiyyar garin Tegina, jihar Neja

- Rahotanni sun bayyana cewa an tsinci gawar yaron ɗan shekara uku kacal a bayan garin Tegina

- Amma har yanzun, hukumar yan sandan jihar Neja bata ce komai game da tsintar gawar yaron da aka yi ba

An gano gawar ɗaya daga cikin ɗaliban islamiyyar da yan bindiga suka sace a garin Tegina, ƙaramar hukumar Rafi, jihar Neja, kamar yadda the nation ta tabbatar.

KARANTA ANAN: Murna Ta Koma Ciki: Hatsari Ya Laƙume Rayukan Matasa 17 Akan Hanyar Dawowa Daga Ɗaurin Aure

Yaron ɗan shekara 3 yana daga cikin ɗalibai 156 da aka sace a islamiyyar Salihu Tanko dake Tegina.

An tsinci gawar ɗalibin ne a wani wuri mara nisa daga garin Tegina, amma har yanzun ba'a gano musabbabin mutuwarsa ba.

Tashin Hankali: An Tsinci Gawar Ɗaya Daga Cikin Ɗaliban Islamiyya da Yan Bindiga Suka Sace a Neja
Tashin Hankali: An Tsinci Gawar Ɗaya Daga Cikin Ɗaliban Islamiyya da Yan Bindiga Suka Sace a Neja Hoto: prumetrics.com
Asali: UGC

A halin yanzu, iyayen wasu daga cikin ɗaliban da aka sace mata guda biyu sun rasa rayuwarsu saboda takaicin abinda ya samu 'yayansu.

Tawagar iyayen ɗaliban sun nuna rashin jin daɗinsu kan yanayin yadda gwamnatin jihar take tafiyar da lamarin kuɓutar da ƴaƴansu.

KARANTA ANAN: Cikakken Bayani: Yadda Yan Bindiga Suka Ƙona Gidan Kwamishinan Jihar Imo

Legit.ng hausa ta gano cewa, mako ɗaya da faruwar lamarin amma har yanzun babu wata tawagar gwamnatin jihar da taje garin domin jajanta musu.

Iyayen yaran sun ce: "Shugaban ƙaramar hukumar su, Ismaila Modibbo, shine kaɗai yake taimakawa wajen fafutukar haɗa kuɗin da yan bindigan suka nema, domin kuɓutar da ɗaliban."

Hukumar yan sandan jihar Neja bata fitar da rahoton gano gawar ɗaya daga cinin ɗaliban ba har yanzun da muke haɗa wannan rahoton.

A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Kai Wani Mummunan Hari a Katsina, Sun Kashe Mutum 6 Tare da Jikkata Wasu da Yawa

Wasu yan bindiga kan mashin 60 sun kai hari ƙauyukan Runka da Kanawa dake ƙaramar hukumar Danmusa, jihar Katsina.

Yan bindigan sun kashe mutum shida tare da jikkata wasu da dama a mummunan harin da suka kai, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel