Murna Ta Koma Ciki: Hatsari Ya Laƙume Rayukan Matasa 17 Akan Hanyar Dawowa Daga Ɗaurin Aure
- Wasu matasan Kano guda 17 sun gamu da ajalinsu a wani hatsari da ya ritsa dasu akan hanyar Zariya zuwa Kano
- Rahotanni sun bayyana cewa matasan sun dawo ne daga ɗaura auren abokin su da suka halarta a Kaduna
- Mutum 11 daga cikinsu sun rasu ne nan take, yayin da ragowar shida suka ce ga garin ku nan bayan an kaisu asibiti
Wasu matasa 17 daga jihar Kano sun gamu da ajalinsu a wani mummunan hatsarin mota da ya ritsa da su akan hanyar Zaria zuwa Kano ranar Asabar.
KARANTA ANAN: Cikakken Bayani: Yadda Yan Bindiga Suka Ƙona Gidan Kwamishinan Jihar Imo
Daily Nigerian ta ruwaito cewa hatsarin ya faru ne da yammacin Asabar lokacin da matasan ke kan hanyar komawa Kano bayan sun halarci ɗaura auren abokin su a Kaduna.
Legit.ng hausa ta gano cewa matasan na cikin wata motar 'Kano Line' lokacin da hatsarin ya faru da su.
Umar Abdullahi, abokin ɗaya daga cikin mamatan, Umar Abba Sherrif, yace ya samu labarin mutuwar abokin nasa da misalin ƙarfe 8:00 na dare.
Yace wacce ta faɗa masa mutuwar ta tabbatar masa da cewa abokin sa ya rasu ne nan take, kamar yadda vanguard ta ruwaito.
Mr. Abdullahi yace takwas daga cikin matasan sun fito ne daga Sani Mainagge, ƙaramar hukumar Gwale ta jihar Kano.
Jaridar daily Nigerian ta gano cewa 11 daga cikin matasan sun rasu ne nan take yayin da sauran 6 suka ƙarisa rasuwa bayan an kaisu asibiti.
KARANTA ANAN: Yan Bindiga Sun Kai Wani Mummunan Hari a Katsina, Sun Kashe Mutum 6 Tare da Jikkata Wasu da Yawa
Har yanzun ba'a gano musabbabin hatsarin ba, kuma an kira lambar kakakin hukumar kare haɗurra na jihar, Muhammad Kangiwa, amma wayarsa a kashe.
A ta'aziyyar da yayi wa iyalan mamatan, Gwamnan Abdullahi Ganduje, a wani jawabi da kakakinsa, Abba Anwar, ya fitar, gwamnan yace:
"Wannan babban rashi ne mai ciwo ga iyalan matasan da kuma mutanen Sani Mainagge, ƙaramar hukumar Gwale inda suka fito, sannan kuma damu baki ɗaya, gwamnati da jama'ar jihar Kano."
Ganduje yace wannan ƙaddara ce ta Allah, kuma shi kaɗai ne zai yafe musu, gwamnan yace: "Muna addu'a Allah SWT ya gafarta musu kurakuransu, yasa aljanna ce makomarsu, Su kuma iyalansu Allah ya basu hakurin jure wannan rashin da suka yi."
A wani labarin kuma Nan Gaba Ƙaɗan Wasu Gwamnonin PDP Zasu Sauya Sheƙa Zuwa APC, Ganduje
Gwamnan Kano , Abdullahi Ganduje, ya bayyana cewa nan gaba kaɗan APC zata yi sabbin gwamnoni daga jam'iyyar PDP
Gwamna Ganduje yace tuni jam'iyya mai mulki ta fara shirye-shiryen tarbar gwamnonin, kamar yadda vanguard ta ruwaito.
Asali: Legit.ng