Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Banka Wuta a Gidan Kwamishinan Jihar Imo

Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Banka Wuta a Gidan Kwamishinan Jihar Imo

- Wasu yan bindiga sun bi dare sun ƙona gidan kwamishinan yaɗa labarai na jihar Imo, Chief Declan Emelumba.

- Rahotanni sun bayyana cewa yan bindigan sun ɓalle kofar gidan sannan suka banka wuta a gidan

- Chief Emelumba, shine ya tabbatar da haka, yace babu kowa a gidan sai mai gadi, kuma basu taɓa shi ba

Wasu yan bindiga sun ƙona gidan kwamishinan yaɗa labarai na jihar Imo, Chief Declan Emelumba, dake ƙaramar hukumar Oru ta gabas a jihar, kamar yadda the nation ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Yan Bindiga Sun Kai Wani Mummunan Hari a Katsina, Sun Kashe Mutum 6 Tare da Jikkata Wasu da Yawa

Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 1:00 na dare, kuma wutar ta cinye dukkan kayayyakin dake cikin gidan baki ɗaya, kamar yadda Pm News ta ruwaito.

Wata majiya ta bayyana cewa yan bindigan sun ɓalla ƙofar gidan, kuma suka cinna wuta ba tare da wata fargaba ba.

Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Banka Wuta a Gidan Kwamishinan Jihar Imo
Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Banka Wuta a Gidan Kwamishinan Jihar Imo Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Kwamishina Chief Emelumba, shine ya tabbatar da faruwar lamarin ga yan jarida.

KARANTA ANAN: Rundunar Yan Sanda Ta Ragargaji Wasu Yan Fashi 5 a Jihar Benuwai

Yace: "Da safiyar yau Lahadi, tsakanin ƙarfe 1:00 zuwa 2:00 na dare, wasu mutane suka kirani daga ƙauyen mu,suka cemun wasu yan bindiga sun kai hari gidana, sun ɓalla ƙofar gidan sannan suka cinna wuta."

"Mai gadin gidan, wanda shi kaɗai ne a wurin ya tsira ba tare da sun cutar da shi ba, amma maharan sun shiga gidan sun ƙona komai dake ciki."

A wani labarin kuma Nan Gaba Ƙaɗan Wasu Gwamnonin PDP Zasu Sauya Sheƙa Zuwa APC, Inji gwamna Ganduje

Gwamnan Kano , Abdullahi Ganduje, ya bayyana cewa nan gaba kaɗan APC zata yi sabbin gwamnoni daga jam'iyyar PDP.

Gwamna Ganduje yace tuni jam'iyya mai mulki ta fara shirye-shiryen tarbar gwamnonin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262