Yan Bindiga Sun Kai Wani Mummunan Hari a Katsina, Sun Kashe Mutum 6 Tare da Jikkata Wasu da Yawa

Yan Bindiga Sun Kai Wani Mummunan Hari a Katsina, Sun Kashe Mutum 6 Tare da Jikkata Wasu da Yawa

- Wasu yan bindiga kan mashin 60 sun kai hari ƙauyukan Runka da Kanawa dake ƙaramar hukumar Danmusa, jihar Katsina

- Yan bindigan sun kashe mutum shida tare da jikkata wasu da dama a mummunan harin da suka kai

- Wani mazaunin garin Kanawa ya tabbatar da harin, yace maharan sun watsa yan garin zuwa cikin daji

Yan bindiga sun kai hari ƙauyukan Runka da Kanawa dake yankin ƙaramar hukumar Ɗanmusa jihar Katsina.

KARANTA ANAN: 2023: Nan Gaba Ƙaɗan Wasu Gwamnonin PDP Zasu Sauya Sheƙa Zuwa APC, Ganduje

Rahoton dailytrust ya nuna cewa aƙalla mutum shida ne suka kashe yayin da suka kai harin.

Wani mazaunin ƙauyen Kanawa, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar, yace maharan sun shigo ƙauyen su da yammacin Asabar, inda suka watsa mutane.

Yan Bindiga Sun Kai Wani Mummunan Hari a Katsina, Sun Kashe Mutum 6 Tare da Jikkata Wasu da Yawa
Yan Bindiga Sun Kai Wani Mummunan Hari a Katsina, Sun Kashe Mutum 6 Tare da Jikkata Wasu da Yawa Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Yace: "Da mukaji ƙarar mashina da yawa sai muka fara gudu don ceton rayuwar mu, amma suka bi suka kamo wasu, suka harbe shida har lahira, suka jikkata wasu."

"A yanzun da nake magana daku bamu daɗe da gama jana'izar mutum shida da suka kashe ba, kuma akwai wasu mutum uku da suka ji munanan raunuka."

"Ɗaya daga cikinsu an kaishi asibitin Katsina, sauran biyun kuma suna nan cikin ƙaramar hukumar Danmusa."

KARANTA ANAN: Rundunar Yan Sanda Ta Ragargaji Wasu Yan Fashi 5 a Jihar Benuwai

Yace yan bindigan sun zo a mashin aƙalla guda 60 da misalin ƙarfe 6:30 na yamma, ance sun ɗauki dabbobi mallakin wata amarya a ƙauyen.

Da aka tuntuɓi kakakin hukumar yan sanda na jihar, SP Gambo Isah, kan lamarin, yace har yanzun DPO na yankin bai kawo musu rahoto ba, amma yayi alƙawarin zai neme shi domin jin abinda ke faruwa.

A wani labarin kuma bayan mutuwar fitaccen malamin majami'ar dukkan ƙasashe, akwai wasu Muhimman Abubuwa 7 da Ya Kamata Ku Sani Game da Marigayi T. B Joshua

Malamin majami'ar dukkan ƙasashe, T. B Joshua ya riga mu gidan gaskiya yana da shekara 57 a duniya, kamar yadda the nation ta ruwaito.

An haifi Joshua ne a ranar 12 ga watan Yuni 1963, ya rasu gab da zagayowar ranar haihuwarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel