Na Sayi Wannan Keken Shekaru 40 Da Suka Wuce Akan N23 Kuma Zan Tuka Shi Har Mutuwa Na: Mutumin Kano

Na Sayi Wannan Keken Shekaru 40 Da Suka Wuce Akan N23 Kuma Zan Tuka Shi Har Mutuwa Na: Mutumin Kano

- Wani dan Najeriya da aka bayyana da suna Ibrahim Dan Maliki ya ce ba shi da niyan jefar da kekensa mai shekara 40

- Mutumin mai shekaru 68 ya bayyana cewa lokacin da ya siya a kan kusan N23, komai na da arha sosai saboda ana iya canza taya a kan farashin N1

- A cewar mahaifin mai yara takwas, zai ci gaba da hawa keken har sai ya mutu, yana mai nuni da cewa ita ce kawai hanyar sa ta saukaka zirga zirga

Don bikin ranar kekuna ta duniya a ranar Alhamis, 3 ga watan Yuni, BBC News Pidgin ta tattauna da wani dan Najeriya, Ibrahim Dan Maliki, wanda ya sayi nasa shekaru 40 da suka gabata.

A hirar da ya yi da jaridar, mutumin ya nuna matukar kaunarsa ga keken kuma ya ce zai hau shi har sai mutuwa ta raba su.

KU KARANTA KUMA: Da dumi: 'Yan bindigga sun kashe mutane 66 a sabon harin da suka kai a kauyuka 8 na Kebbi

Na Sayi Wannan Keken Shekaru 40 Da Suka Wuce Akan N23 Kuma Zan Tuka Shi Har Mutuwa Na: Mutumin Kano
Na Sayi Wannan Keken Shekaru 40 Da Suka Wuce Akan N23 Kuma Zan Tuka Shi Har Mutuwa Na: Mutumin Kano Hoto: @bbcnewspidgin
Asali: Twitter

Abubuwa na da arha

Mutumin ya lura cewa ya sayi keken a kusan N23, yana mai bayyana cewa murnar da ta kawo masa a ranar sayan ba ta da iyaka.

Ibrahim ya bayyana cewa canza taya ya kasance kasa da N1 amma lamarin ya sha bamban a yanzu saboda zai kashe N2000 don yin hakan.

KU KARANTA KUMA: Haramta Twitter: FG ta bayyana dalilai 3 da suka sa aka dakatar da kafar sadarwar

Dukanmu ke da hanyar

Dangane da gwagwarmayarsa da masu ababen hawa, mutumin mai yara takwas ya ce haƙuri ya kasance kayan aikinsa. Ya kara da cewa abin da masu motoci basu sani ba shine hanyar ta kowa ce.

A wani hoto da jaridar ta yada a shafinta na Instagram, an ga mutumin dauke da buhu a daure akan keken.

Kalli wallafar a kasa:

Ga wasu daga cikin martanin jama'a kan labarinsa:

sunnydyoung ya ce:

"Keke ba ya mutuwa ina taya ka farin ciki saboda ka ji daɗinka tsoho."

julyanah__ ta ce:

"Ba na bukatar karanta cikakken labarin don sanin cewa shi dan Kano ne."

franky_burna ya ce:

"Bikin shirme."

A wani labarin, wani saurayi yayi bikin zagayowar ranar haihuwarshi cikin salon da ba zai yi saurin mantawa da shi ba.

Mai bikin, a cikin bidiyon da @kingtundeednut ya wallafa a shafin Instagram ya kayatar da wurin taron zagayowar ranar haihuwar nasa cikin shiga na kasaita.

Saurayin mai suna Ismail Ganiya ya yi ado da shadda tare da sanya tabarau mai duhu yayin da abokan sa ke take masa baya cikin shiga makamancin nasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel