Haramta Twitter: FG ta bayyana dalilai 3 da suka sa aka dakatar da kafar sadarwar

Haramta Twitter: FG ta bayyana dalilai 3 da suka sa aka dakatar da kafar sadarwar

Biyo bayan dakatarwar da aka yi wa kamfanin Twitter a Najeriya, gwamnatin tarayya ta bayyana dalilan da suka sa aka dakatar da ayyukan shafin.

KU KARANTA KUMA: Kisan Gulak: Fargaba a APC yayin da jam’iyyar reshen Adamawa ta aika gagarumin sako ga Gwamna Uzodimma

Haramta Twitter: FG ta bayyana dalilai 3 da suka sa aka dakatar da kafar sadarwar
Haramta Twitter: FG ta bayyana dalilai 3 da suka sa aka dakatar da kafar sadarwar Hoto: @FMICNigeria
Asali: Facebook

Ministan labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed, a cikin wata sanarwa a ranar Juma'a, 4 ga Yuni, a Abuja ya bayyana cewa:

1. An dakatar da amfani da shafin Twitter saboda maslahar Najeriya

2. Gwamnati ta zargi shafin sada zumuntar da yin kafar ungulu ga ka'idar kasancewar kamfanonin Najeriya

3. Ministan ya kuma bayyana cewa dakatarwar na daga cikin dokokin gudanarwar hukumar kula da gidajen rediyo da talbijin ta ƙasar NBC na dukka OTT da kafofin sada zumunta a Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Dakatar Da Twitter: Shehu Sani Ya Bayyana Hanya Mafi Sauki Don Hawa Twitter

Dakatar da ayyukan Twitter a Najeriya na zuwa ne jim kadan bayan da gwamnatin tarayya ta soki katafaren kamfanin na sada zumunta kan share wani rubutu da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wanda ya yi gargadi kan tsauraran matakai a kan masu ballewa.

Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed, a ranar Laraba, 2 ga Yuni, ya zargi shafin na dada zumunta da nuna son kai a kan batutuwan da suka shafi lamuran cikin gida na Najeriya.

Ya ce akwai ayar tambaya a rawar da Twitter ke takawa kuma Najeriya ba za ta yarda a yaudare ta ba.

A wani labarin, kamfanonin sadarwa a Najeriya kamar MTN, Glo, Airtel da 9mobile sun fara rufe amfani da damar shiga dandalin sada zumunta twitter, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kamfanonin sun ce sun samu saƙon umarni daga hukumar sadarwa ta ƙasa NCC cewa su tsayar da damar shiga twitter a ƙasa biyo bayan umarnin gwamnatin tarayya na dakatar da shafin.

Yan Najeriya masu amfani da twitter sun wayi garin ranar Asabar ba tare da samun damar amfani da shafinsu na twitter ba, yayin da wasu ke amfani da wata manhajar sadarwa domin shiga shafin su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel