Bidiyon ruwan kudi da aka yi yayin da wani matashi yayi shigar kasaita a wajen bikin zagayowar haihuwarsa
- Mabiya shafin soshiyal midiya sun tofa albarkacin bakunansu yayin da wani matashi yayi shigar kasaita a wajen bikin zagayowar ranar haihuwarsa
- Matashin mai suna Ismail Ganiya ya shiga dakin tsaron da jami’in tsaro sannan ana ta yi masa yayyafin kudi yayinda yake tafiya zuwa mazauninsa
- An gano abokansa suna take masa baya tamkar wani sarki har sai da ya kai wajen da aka tanada domin zaman shi a cikin wani bidiyo da ke yawo
Wani saurayi yayi bikin zagayowar ranar haihuwarshi cikin salon da ba zai yi saurin mantawa da shi ba.
Mai bikin, a cikin bidiyon da @kingtundeednut ya wallafa a shafin Instagram ya kayatar da wurin taron zagayowar ranar haihuwar nasa cikin shiga na kasaita.
KU KARANTA KUMA: Haramta Twitter: FG ta bayyana dalilai 3 da suka sa aka dakatar da kafar sadarwar
Saurayin mai suna Ismail Ganiya ya yi ado da shadda tare da sanya tabarau mai duhu yayin da abokan sa ke take masa baya cikin shiga makamancin nasa.
An yiwa Ganiya likin kudade yayin da yake a hanyarsa ta shigowa dakin taron. An kuma gano wani sanye da kayan tsaro a bayansa.
Lamarin ya faru ne a jihar Katsina.
KU KARANTA KUMA: Kisan Gulak: Fargaba a APC yayin da jam’iyyar reshen Adamawa ta aika gagarumin sako ga Gwamna Uzodimma
‘Yan Najeriya sun yi martani ga bidiyon
Bidiyon ya ba 'yan Najeriya da dama dariya yayin da suka yi martani masu ban dariya da kuma ba da bayanan abin da ya faru.
@officialmorientez ya ce:
"Ina jin alkalamin na sanya wa mutane hannu ne a karshen sashin."
@sneezymankind ya yi martani:
"Bikin zagayowar ranar haihuwa na biliyoyin Naira wanda Dorime ya dauki nauyi."
@scoobynero ya rubuta:
"Makiyaya a lokacin da suka yanke shawarar hutawa da zuwa shakatawa."
A wani labarin, shahararren mawaki, Naira Marley ya bayyana cewa zai yi zaman jira don rera sabuwar wakar taken kasa bayan yanke shawarar sauya sunan Najeriya zuwa Hadaddiyyar Jamhuriyar Afirka (UAR).
A cewar rahotanni, Adeleye Jokotoye, kwararre kan haraji, ya gabatar da shawarar ga kwamitin a taron sauraron kararrakin yankin Kudu maso Yamma da ke Legas a ranar Laraba, 2 ga Yuni, 2021, jaridar Pulse ta ruwaito.
Yayin da yake gabatar da wannan shawara, ya ce sunan Najeriya turawan mulkin mallaka ne suka tilastawa kasar kuma ya kamata a canza shi.
Asali: Legit.ng