Da dumi: 'Yan bindiga sun kashe mutane 66 a sabon harin da suka kai a kauyuka 8 na Kebbi

Da dumi: 'Yan bindiga sun kashe mutane 66 a sabon harin da suka kai a kauyuka 8 na Kebbi

- 'Yan bindiga sun halaka mutane 66 a wani hari da suka kai karamar Hukumar Danko-Wasagu da ke Jihar Kebbi

- Rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa daga kakinta, DSP Nafiu Abubakar

- Lamarin ya afku ne ranar Alhamis a kauyuka a kauyukan Koro, kimpi, Gaya, Dimi, Zutu, Rafin Gora da Iguenge

‘Yan sanda a Jihar Kebbi sun ce ‘yan bindiga sun kashe mutum 66 a karamar Hukumar Danko-Wasagu da ke Jihar Kebbi.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Nafiu Abubakar, ya ce kisan gillar ya faru ne a ranar Alhamis a kauyuka takwas na karamar hukumar, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Gwamnan Najeriya Ya Aika Sako Ga Buhari, Ya Bayyana Dalilai 5 Da Zai Sa A Janye Dakatarwar Da Aka Yiwa Twitter

Da dumi: 'Yan bindigga sun kashe mutane 66 a sabon harin da suka kai a kauyuka 8 na Kebbi
Da dumi: 'Yan bindigga sun kashe mutane 66 a sabon harin da suka kai a kauyuka 8 na Kebbi Hoto: Kebbi State Government of Nigeria
Asali: Facebook

A cewarsa, duk da cewa rundunar na ci gaba da kirga yawan wadanda suka mutu, amma tuni hukumar 'yan sanda ta jihar ta aike da wasu jami'anta zuwa yankin.

Ya ce:

"Kisan ya faru ne a kauyukan Koro, kimpi, Gaya, Dimi, Zutu, Rafin Gora da Iguenge, duk a karamar hukumar Danko / Wasagu ta jihar Kebbi."

Jaridar ta tattaro cewa akasarin mutanen kauyukan da abin ya shafa sun tsere zuwa garin Riba da ke kusa domin tsira.

KU KARANTA KUMA: Bidiyon ruwan kudi da aka yi yayin da wani matashi yayi shigar kasaita a wajen bikin zagayowar haihuwarsa

A wani labarin, 'Yan bindiga sun nemi a biya su Naira miliyan 200 kudin fansa kafin su sako daliban Islamiyya 156 da aka sace a jihar Neja.

A ranar 27 ga watan Mayu, 'yan bindiga sun kai hari makarantar Salihu Tanko Islamiyya da ke garin Tegina, karamar hukumar Rafi, suka yi awon gaba da wasu 'yan makaranta.

Da farko 'yan fashin sun nemi kudin fansa na naira miliyan 110 kan daliban da aka sace.

Sai dai kuma, lamarin ya dauki sabon salo domin 'yan fashin sun daukaka bukatar su zuwa Naira miliyan 200, jaridar The Cable ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel