Mazauna garin Gauraka na jihar Neja sun tsere sun bar gidajensu yayinda aka ceto mutum 20 da aka sace

Mazauna garin Gauraka na jihar Neja sun tsere sun bar gidajensu yayinda aka ceto mutum 20 da aka sace

- Rahotanni sun nuna cewa mazauna garin Gauraka da ke jihar Neja sun kauracewa gidajensu saboda tsoron garkuwa da su

- An tattaro cewa wasun su kan dawo gida da safe sannan su tsere zuwa wasu garuruwan da daddare domin kwana

- Hakan na faruwa ne duk da cewar jami'an tsaro sun yi nasarar ceto wasu mutum 20 da aka yi garkuwa da su a garin

Har yanzu mazauna garin Gauraka, na jihar Neja, basa kwana a cikin gidajensu saboda tsoron sace su yayin da wasu kuma gaba daya suka koma wasu wuraren a matsayin masu haya.

Wannan na faruwa har bayan wasu jerin samame da rundunar tsaro ta hadin gwiwa suka kai maboyar masu satar mutane a dajin Apo da ke gefen gari.

An tattaro cewa jami’an tsaro sun yi nasarar ceto kimanin mazauna yankin 20 da aka sace a wasu hare-hare biyu da aka kai wa garin kwanaki biyar da suka gabata.

Mazauna garin Gauraka na jihar Neja sun tsere sun bar gidajensu yayinda aka ceto mutum 20 da aka sace
Mazauna garin Gauraka na jihar Neja sun tsere sun bar gidajensu yayinda aka ceto mutum 20 da aka sace Hoto: @channelstv
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Majalisar dattijai yi juyayin mutuwar Ibrahim Attahiru da Ahmed Gulak

A ranar Litinin da ya gabata ne ɗaruruwan matasa a kusa da yankin suka toshe babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna, suna nuna rashin amincewa da jerin sace-sacen mutane a can, kamar yadda gidan talbijin din Channels ta ruwaito.

Wani mazaunin garin, Musa Abubakar, yayin da yake zantawa da jaridar Daily Trust, ya ce mazauna Unguwar Boko da Barau sun daina kwana a yankin saboda tsoron afkuwar hari, suna dawowa ne kawai da rana sannan su tsere da yamma.

Ya ce bayan zanga-zangar da ta gabata, jami'an tsaro sun kewaye maboyar 'yan bindigar, kuma sun ceto mutane 20 yayin da yan bindigar suka gudu.

Ya ce kafin ci gaban, masu satar mutanen suna shirin kai hare-hare a tsakiyar garin.

Wani mazaunin yankin, Ya’u Ahmed, ya kuma koka cewa wasu mazauna garin sun riga sun koma wasu wurare ko dai a matsayin masu haya ko kuma su zauna tare da danginsu.

KU KARANTA KUMA: Ana zanga zanga a jihohin Najeriya hudu kan rashin tsaro da rashin shugabanci mai inganci

An tattaro cewa yayin da jami'an tsaron suka yi nasarar fatattakar maharan daga sansanoninsu, a daya bangaren kuma, 'yan bindigar, suna ci gaba da damun mutanen da aka ceto ta hanyar kiran waya suna neman a aika musu da kudi, ko kuma su sake sace su.

Jaridar ta ce bata samu jin ta bakin kwamandan yan sandan Suleja, ACP Sani Badarawa ba, domin bai samu amsa kiran waya ba.

A wani labarin, wasu yan bindiga kimanin 20 sun kutsa Alaafia Estate a Orogun, Ibadan, babban birnin jihar Oyo, sun raba mutane da kayayyakinsu da kudadensu, The Punch ta ruwaito.

The Nation ta ruwaito cewa wasu daga cikin yan bindigan sun yi amfani da na'urar tura kudade na POS wurin sace kudade daga hannun wadanda ba su da tsabar kudi a hannunsu.

An ce sun tafi da katin ATM din wasu daga cikin mutanen tare da lambar sirri ta PIN dinsu domin su cire kudaden a yayin da suka fuskanci matsala ta sabis.

Asali: Legit.ng

Online view pixel