Sabon Salo: 'Yan fashi sun fara zuwa sata gidajen mutane da na'urar POS

Sabon Salo: 'Yan fashi sun fara zuwa sata gidajen mutane da na'urar POS

- Wasu yan bindiga sun afka gidajen mutane a Alaafia Estate a Orogun, Ibadan sun musu fashi

- Baya ga kwace tsabar kudade da wasu kaya, yan bindigan sun yi amfani da POS wurin karbar kudade

- Mai magana da yawun yan sandan jihar ya tabbatar da lamarin inda ya ce yan sanda sun fatattaki yan bindigan

Wasu yan bindiga kimanin 20 sun kutsa Alaafia Estate a Orogun, Ibadan, babban birnin jihar Oyo, sun raba mutane da kayayyakinsu da kudadensu, The Punch ta ruwaito.

The Nation ta ruwaito cewa wasu daga cikin yan bindigan sun yi amfani da na'urar tura kudade na POS wurin sace kudade daga hannun wadanda ba su da tsabar kudi a hannunsu.

Sabon Salo: 'Yan bindiga sun afka gidajen mutane a sunyi fashi da POS
Sabon Salo: 'Yan bindiga sun afka gidajen mutane a sunyi fashi da POS. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Da Duminsa: Buhari Ya Cire Shugaban NEMA, Ya Maye Gurbinsa Da Habib

An ce sun tafi da katin ATM din wasu daga cikin mutanen tare da lambar sirri ta PIN dinsu domin su cire kudaden a yayin da suka fuskanci matsala ta sabis.

Wakilin majiyar Legit.ng ya ce kimanin gidaje 25 yan bindigan suka shiga suka yi wa fashin.

Yan bindigan, cikin fushi sun lalata kayayaki da dama a gida na 25, inda suka zargi wasu daga cikin yan gidan da lekensu suna kallon yadda suke fashin wasu gidajen.

An ruwaito cewa daga bisani an sanar da jami'an yan sanda abin da ke faruwa kuma da isowarsu yan bindigan sun cika wandunansu da iska sun tsere.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, Mr Adewale Osifeso, ya ce an sanar da yan sandan misalin karfe 3 na dare kuma sun tura wasu jami'ansu wurin.

KU KARANTA: Za a Fara Bawa Malaman Makarantun Allo Shaidar Karatu Ta ‘NCE’ a Kaduna

Ya ce, "Da ganin yan sanda, yan bindigan suka tsere bayan gumurzu da suka yi. A yayin hakan, an kwato bindiga pistol da adduna uku da jaka dauke da tufafi da layukan waya masu yawa."

Ya ce ana cigaba da bibiyan sahun yan bindigan domin a kamo su.

A wani labari daban, Gwamnatin jihar Kano ta hana shan sigari a bainar jama'a domin yaki da annobar cigari a yayin da ake samun kimanin mutane 16,100 da ke mutuwa duk shekara daga matsaloli masu alaka da cigari, Daily Trust ta ruwaito.

A wani mataki na habbaka lafiya da rayuwar al'umma a jihar na Kano, gwamnatin jihar ta ce ta ware kudade da dama domin yaki da cututtuka marasa saurin yaduwa kamar hawan jini, sikila, asma da ciwon huhu masu alaka da shan cigari da sauransu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel