Majalisar dattijai ta yi juyayin mutuwar Ibrahim Attahiru da Ahmed Gulak
- Majalisar dattawa ta yi makokin tsohon shugaban hafsan sojin kasar, Laftanar Janar Ibrahim Attahiru
- Hakazalika a zamanta na yau Talata, 1 ga watan Yuni, majalisar ta kuma yi alhinin mutuwar Ahmed Gulak wanda aka kashe a jihar Imo
- Daga nan zauren majalisar ya yi tsit na mintina daddaya domin karrama mamatan
Majalisar dattijai a ranar Talata, 1 ga watan Yuni, ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta dunga tunawa da marigayi Babban Hafsan Sojojin kasar, Laftanar Janar Ibrahim Attahiru.
Hakanan majalisar ta yi shiru na minti guda don girmama mamacin.
KU KARANTA KUMA: Ana zanga zanga a jihohin Najeriya hudu kan rashin tsaro da rashin shugabanci mai inganci
Wannan ya biyo bayan wani oda da shugaban kwamitin majalisar dattijai kan Soja, Sanata Ali Ndume ya gabatar, jaridar Punch ta ruwaito.

Asali: Twitter
Har ila yau, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ovie Omo-Agege, ya janyo hankalin majalisar dattijan ga batun marigayi tsohon hadimin tsohon shugaban kasa, Ahmed Gulak, wanda ya ce an kashe shi yayin da yake kan aikin kasa a Owerri, babban birnin jihar Imo.
Omo-Agege ya yi Allah wadai da kisan Gulak, wanda ya ce yana daya daga cikin masu ba da shawara da Kwamitin Majalisar Dattawa kan Binciken Kundin Tsarin Mulki ya dauke su aiki a kan gyaran da ‘yan Nijeriya ke neman yi wa Kundin Tsarin Mulki na 1999.
Dangane da bukatar mataimakin kakakin majalisar, Majalisar Dattawa ta yi Allah wadai da kisan kuma sun yi tsit na minti daya don girmama shi.
KU KARANTA KUMA: PDP ta yi magana a kan kisan Ahmed Gulak, ta ambaci wanda ya kamata a rike
A gefe guda, mun ji cewa Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya nemi amincewar majalisa kan naɗin sabon shugaban rundunar sojin ƙasa, Mejo Janar Farouk Yahaya, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata takarda da shugaban ya aike wa majalisar, kuma shugaban majalisar dattijai, Ahmad Lawan, ya karanta a zaman su na yau Talata.
Shugaba Buhari ya roƙi sanatocin da su duba kuma su amince da buƙatar da ya turo musu cikin hanzari.
Asali: Legit.ng