Ana zanga zanga a jihohin Najeriya hudu kan rashin tsaro da rashin shugabanci mai inganci

Ana zanga zanga a jihohin Najeriya hudu kan rashin tsaro da rashin shugabanci mai inganci

- Kungiyoyin fararen hula (CSOs) da sauran su sun nuna rashin jin dadinsu game da karuwar talauci a kasar

- Kungiyoyin sun dauki kwalayen sanarwa dauke da rubutu daban-daban yayin da suke rera wakokin da ke isar da sakon su ga gwamnati

- Jagoran zanga-zangar ta Legas, Femi Falana, ya bayyana dalilin da ya sa yake da muhimmanci a wadata talakawa

- Lauyan ya nuna cewa akwai alaƙa tsakanin talauci da rashin tsaro

Mambobin kungiyoyin farar hula sun shirya zanga-zangar lumana a jihohin Abuja, Lagos, Osun, da Edo kan rashin tsaro da rashin tsari a kasar.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa wasu kungiyoyin da suka shiga zanga-zangar sun hada da masu rajin kare hakkin dan adam, kungiyoyin farar hula (CSOs), kungiyoyin kwadago, kungiyoyin matasa, da sauransu.

KU KARANTA KUMA: PDP ta yi magana a kan kisan Ahmed Gulak, ta ambaci wanda ya kamata a rike

Ana zanga zanga a jihohin Najeriya hudu kan rashin tsaro da rashin shugabanci mai inganci
Ana zanga zanga a jihohin Najeriya hudu kan rashin tsaro da rashin shugabanci mai inganci Hoto: @theonly1acre
Asali: Twitter

Zanga-zangar da aka yi a Legas karkashin jagorancin lauya mai fafutuka, Femi Falana, an yi mata inkiya da Ranar daukar matakin kasa kan Rashin Tsaro a Najeriya.

Shi da sauran masu zanga-zangar lumana sun ɗauki kwalayen sanarwa dauke da rubutu daban-daban.

Lauyan da tawagarsa sun yi tattaki zuwa sakatariyar jihar Legas da ke Alausa, Ikeja, babban birnin jihar a ranar Litinin, 31 ga watan Mayu.

'Yan majalisar dokokin jihar ne suka tarbe su, gidan talbijin na Channels ta ruwaito.

Falana ya shawarci majalisar dokokin Legas da ta yi dokokin da za su kara yawan kasafin kudin talakawa.

Ya bayyana cewa ba za a iya tabbatar da zaman lafiya a kasar ba idan ba a samar wa talakawa bukatun yau da kullun ba.

KU KARANTA KUMA: Sanin wanda ya kashe Ahmed Gulak: Gwamna Wike ya caccaki gwamna Uzodinma da yi masa kashedi

Falana ya ce: “Yanzu ya bayyana a kasarmu cewa idan babu zaman lafiya ga talakawa, ba za a iya samun zaman lafiya ga masu arziki ba. Ga wadanda suke son yakar 'yan ta'adda da ta'addanci, dole ne mu sanya dukkan yaranmu a makaranta.”

A wani labarin, Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya nemi amincewar majalisa kan naɗin sabon shugaban rundunar sojin ƙasa, Mejo Janar Farouk Yahaya, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata takarda da shugaban ya aike wa majalisar, kuma shugaban majalisar dattijai, Ahmad Lawan, ya karanta a zaman su na yau Talata.

Shugaba Buhari ya roƙi sanatocin da su duba kuma su amince da buƙatar da ya turo musu cikin hanzari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel