PDP ta yi magana a kan kisan Ahmed Gulak, ta ambaci wanda ya kamata a rike

PDP ta yi magana a kan kisan Ahmed Gulak, ta ambaci wanda ya kamata a rike

- PDP tayi wasu kakkausan zargi a kan APC biyo bayan kisan Ahmed Gulak da kuma rashin tsaro a kasar

- Kola Ologbondiyan, mai magana da yawun PDP a cikin wani kakkausar sanarwa ya caccaki jam'iyya mai mulki da mambobinta kan halin da kasar ke ciki

- Jam’iyyar APC a wata sanarwa daban kwanakin baya ta yi gagarumin zargi kan PDP game da halin tsaron Najeriya

Jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) ta yi zargin cewa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da shugabanninta ke da alhakin kisan shahararren dan siyasar, Ahmed Gulak.

Jam’iyyar ta yi wannan zargin ne a cikin wata sanarwa da ta fitar ta bakin kakakinta, Kola Ologbondiyan ta shafin Facebook a ranar Litinin, 31 ga watan Mayu.

KU KARANTA KUMA: Kada ku siyasantar da kisan Gulak, gwamnonin arewa sun gargadi ‘yan Najeriya

PDP ta yi magana a kan kisan Ahmed Gulak, ta ambaci wanda ya kamata a rike
PDP ta yi magana a kan kisan Ahmed Gulak, ta ambaci wanda ya kamata a rike Hoto: @L_man
Asali: Twitter

Ologbondiyan ya yi ikirarin cewa binciken da jam'iyyarsa ta yi ya nuna cewa mutuwar Gulak da sauran kashe-kashen da ake yi a kasar ya kamata a dora alhakinsu kan jam'iyyar mai mulki.

Ya ce jam'iyyar APC ta sanya siyasa cikin mummunar kisan gillar da aka yi wa fitaccen dan Najeriya kamar Gulak, lamarin da ya faru a jihar da take karkashinta, maimakon yin tir da abin da karfi.

Jam’iyyar ta PDP ta kuma zargi mambobin APC da samun alaka da wadanda ke haifar da rashin tsaro a kasar.

Ya ce:

“Jam'iyyarmu ta dage kan cewa duk wata hujja da za a gabatar ta nuna cewa APC da shugabanninta suna aiwatar da ajandarsu da nufin lalata kasarmu ta hanyar amfani da harshensu na rashin mutunci, manufofin rarrabuwar kai, cin zarafin mutane, cin zarafin 'yancin dan adam, rashin kula da tunaninmu na kasa da kuma diban 'yan ta'adda da ‘yan fashi, wadanda suke haifar da kashe-kashe da tashe-tashen hankula da rashin jituwa a fadin kasarmu."

Kakakin na PDP ya yi zargin cewa mambobin jam’iyya mai mulki na boye mutanen da ke nuna soyayyarsu ga ’yan fashi da’ yan ta’adda.

KU KARANTA KUMA: A ƙarshe dan Gulak ya magantu, ya bayyana kalmomin mahaifinsa na ƙarshe

Ga martanin wasu yan Najeriya kan lamarin.

David Osagiede ya ce:

"Buhari ba ya kokarin ko kadan, a takaice, Buhari babban karkiya ne da nauyi a wuyan ‘yan Najeriya."

Baba Mohammed ya yi martani:

"Babu abunda PDP dinnan ke tabukawa na kwarai. Kodayaushe jawabin labarai maimakon bayar da shawara don samun mafita mai dorewa."

Tunde Ezomon ya ce:

"APC na girbe abunda suka shuka ne."

Olufemi Vaughan ya yi martani:

"PDP ba zai sake faruwa ba a Najeriya."

A gefe guda, Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas ya ce Gwamna Hope Uzodinma yana nuna yanayi kamar cewa ya san halin da ake ciki game da mutuwar Ahmed Gulak ta hanyar bayyana kisan a matsayin kisan siyasa.

Gwamnan na jihar ta Ribas ya bayyana hakan ne a cikin wata hira da ya yi da gidan Talabijin na Channels a ranar Litinin, 31 ga Mayu.

Ya nemi takwaran nasa na jihar Imo da ya ba jami’an tsaro damar kammala bincikensu kafin a danganta kisan da aka yi wa jigon na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a matsayin kisan siyasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel