Da Dumi-Ɗumi: Buhari Ya Nemi Majalisa Ta Tabbatar da Nadin Sabon COAS, Manjo Janar Yahaya

Da Dumi-Ɗumi: Buhari Ya Nemi Majalisa Ta Tabbatar da Nadin Sabon COAS, Manjo Janar Yahaya

- Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya nemi majalisar dattijai data tabbatar da sabon shugaban rundunar sojin ƙasa, Mejo Janar Farouk Yahaya

- Shugaban majalisar, sanata Ahmad Lawan, shine ya karanta wasiƙar shugaban a zamanta na yau Talata

- Buhari ya naɗa Janar Farouk Yahaya ne biyo bayan mutuwar marigayi Janar Ibarahim Attahiru

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya nemi amincewar majalisa kan naɗin sabon shugaban rundunar sojin ƙasa, Mejo Janar Farouk Yahaya, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Shugaban Islamiyyar da Aka Sace Ɗalibanta a Neja Yayi Magana da Yan Bindiga Ta Wayar Tarho

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata takarda da shugaban ya aike wa majalisar, kuma shugaban majalisar dattijai, Ahmad Lawan, ya karanta a zaman su na yau Talata.

Da Dumi-Ɗumi: Buhari Ya Nemi Majalisa Ta Tabbatar da Nadin Sabon COAS, Manjo Janar Yahaya
Da Dumi-Ɗumi: Buhari Ya Nemi Majalisa Ta Tabbatar da Nadin Sabon COAS, Manjo Janar Yahaya Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Shugaba Buhari ya roƙi sanatocin da su duba kuma su amince da buƙatar da ya turo musu cikin hanzari, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Wani ɓangaren takardar yace: "Na turo muku domin ku tabbatar da naɗin Mejo Janar Farouk Yahaya a matsayin shugaban rundunar sojin ƙasa ta Najeriya."

"Tarihin karatunsa da nasarorinsa duk suna haɗe da wannan takardar, ina fatan majalisa zata duba kuma ta amince cikin hanzari."

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa Mejo Janar Farouk Yahaya a matsayin sabon shugaban rundunar sojin ƙasa biyo bayan mutuwar Marigayi Ibrahim Attahiru a cikin watan Mayu.

KARANTA ANAN: Rundunar Yan Sanda Ta Damƙe Mambobin IPOB Shida a Ebonyi, Ta Kwato Makamai a Hannun Su

Tsohon COAS ɗin, Ibrahin Attahiru ya rasa rayuwarsa ne a wani hatsarin jirgin sama da ya rutsa da shi a Kaduna, tare da wasu manyan jami'an soji 10.

A wani labarin kuma Gwamna Matawalle Ya Dakatar da Sarki, Hakimi Bisa Zargin Taimaka Wa Yan Bindiga, Ya Naɗa Kwamitin Bincike

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya dakatad da Sarkin Ɗansadau, Hussaini Umar, da hakimin Nasarawa Mailayi, Bello Wakkala, bisa zarginsu da hannu a ayyukan yan bindiga.

A cewar jawabin da mai taimaka wa gwam nan kan yaɗa labarai, Zailani Baffa, ya fitar yace dakatarwar zata fara aiki nan take, kamar yadda daily Nigerian ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel