Da dumi-dumi: Mutane da dama sun jikkata yayinda abun fashewa ya tashi a kasuwar Port Harcourt

Da dumi-dumi: Mutane da dama sun jikkata yayinda abun fashewa ya tashi a kasuwar Port Harcourt

- Wani abun fashewa ya tashi a wasu sassa na kasuwar mile 3 a karamar hukumar Port Harcourt, jihar Ribas

- Mutane da dama sun jikkata yayinda lamarin ya haifar da tsoro a tsakanin al’umman yankin

- Rundunar yan sanda a jihar ta ce jami’anta na hanyar zuwa wajen don tabbatar da lamarin

Wani abun fashewa ya tashi a wasu sassa na kasuwar mile 3 a karamar hukumar Port Harcourt, jihar Ribas jaridar The Nation da Vanguard suka ruwaito.

Lamarin, wanda ya faru da misalin karfe 6:30 na safiyar ranar Litinin, 31 ga watan Mayu, ya sanya mutane musamman a tashar motoci ta Mile 3 gudu zuwa wurare daban-daban don tsiratar da rayuwarsu.

KU KARANTA KUMA: Matasan Zamfara sun toshe babbar hanya, sun lalata ababen hawa a wata mummunar zanga-zanga da suke gudanarwa

Da dumi-dumi: Mutane da dama sun jikkata yayinda abun fashewa ya tashi a kasuwar Port Harcourt
Da dumi-dumi: Mutane da dama sun jikkata yayinda abun fashewa ya tashi a kasuwar Port Harcourt
Asali: Original

Kodayake ba a rasa rai ba, amma rahotanni sun ce mutane da yawa sun ji rauni.

Wata majiya a cikin kasuwar ta ce fashewan abun ya haifar da tsoro a yankin.

Kakakin rundunar 'yan sanda na Ribas, SP. Nnamdi Omoni, ya ce ‘yan sanda na kan hanyarsu ta zuwa yankin don tabbatar da faruwar lamarin.

KU KARANTA KUMA: 'Yan bindiga sun nemi a biya kudin fansa naira Miliyan 50 domin sakin wadanda aka sace a Neja

A wani labarin, mun ji cewa Ƴan bindiga sun halaka kimanin mutane 12 a harin da suka kai a wasu garuruwa a ƙaramar hukumar Ako a jihar Benue, Daily Trust ta ruwaito.

Shaidun gani da ido sun ce an kai hare-haren ne a lokuta guda daga daren ranar Asabar da Safiyar Lahadi a Tologa, Ndi-Obasi, Odoken duk a mazabar Ekile a ƙaramar hukumar Ado.

Shugaban karamar hukumar Ado, James Oche, ya shaidawa manema labarai a Makurdi a wayan tarho cewa an kashe mutane 12 yayin hare-haren da aka kai a ƙauyuka biyar a garin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel