Rayuka 12 Sun Salwanta a Sabin Hare-Haren Da Aka Kai a Ado

Rayuka 12 Sun Salwanta a Sabin Hare-Haren Da Aka Kai a Ado

- An kashe mutane goma sha biyu a sabbin hare-haren da aka kai ƙaramar hukumar Ako a Benue

- Wasu majiyoyi da abin ya faru a idonsu sun ce an kai hare-haren ne a daga daren ranar Asabar zuwa safen Lahadi

- James Oche, shugaban ƙaramar hukumar Ako ya tabbatar da harin yana mai cewa ramuwar gayya ne

Ƴan bindiga sun halaka kimanin mutane 12 a harin da suka kai a wasu garuruwa a ƙaramar hukumar Ako a jihar Benue, Daily Trust ta ruwaito.

Shaidun gani da ido sun ce an kai hare-haren ne a lokuta guda daga daren ranar Asabar da Safiyar Lahadi a Tologa, Ndi-Obasi, Odoken duk a mazabar Ekile a ƙaramar hukumar Ado.

Rayyuka 12 Sun Salwanta a Sabin Hare-Haren Da Aka Kai a Ado
Rayyuka 12 Sun Salwanta a Sabin Hare-Haren Da Aka Kai a Ado. Hoto: @Vanguardngr
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Da Ɗuminsa: Ƴan Bindiga Sun Sace Ɗalibai 200 a Makarantar Islamiyya a Neja

Shugaban karamar hukumar Ado, James Oche, ya shaidawa manema labarai a Makurdi a wayan tarho cewa an kashe mutane 12 yayin hare-haren da aka kai a ƙauyuka biyar a garin.

Oche ya yi ikirarin cewa hare-haren na ramuwar gayya ne bayan wasu da ake zargin yan IPOB ne daga jihar Ebonyi suka tsallako Benue suka kashe wani dattijon bafulani mai suna Muhammad Isah.

"Ina zargin makiyayan sun yi ramuwar gayya ne saboda ƴan IPOB daga jihar Ebonyi sun tsallako sun shigo Ado sun kashe wani dattijon bafulani Isah Muhammad da ke zaune a wani gari da ke da iyaka da karamar hukumar Ohakwu," in ji shi.

KU KARANTA: An Kama Budurwa Da Saurayi Da Ke Safarar Miyagun Ƙwayoyi Ta Intanet a Abuja

Da aka tuntube shi, mai magana da yawun rundunar yan sanda jihar Benue, DSP Catherine Anene, bai amsa wayarsa ba da saƙon kar ta kwana da aka aike masa yayin haɗa wannan rahoton.

A wani labarin daban, 'yan sanda a birnin tarayya Abuja sun kama Ahmad Isah, mai rajin kare hakkin bil adama kuma dan jarida, saboda shararawa wata mari da ake zargi da cin zarafin wata yarinya.

Isah, wanda aka fi sani da 'Ordinary President' ya dade yana gabatar da wani shirin rediyo da talabijin mai suna "Brektet Family".

Al'umma sun yi korafi a kansa ne bayan an gan shi cikin wani faifn bidiyo da BBC Africa Eye ta wallafa yana marin wata mata da ake zargin da cinnawa yar dan uwanta wuta a kai kan zarginta da maita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel