Matasan Zamfara sun toshe babbar hanya, sun lalata ababen hawa a wata mummunar zanga-zanga da suke gudanarwa

Matasan Zamfara sun toshe babbar hanya, sun lalata ababen hawa a wata mummunar zanga-zanga da suke gudanarwa

- Fusatattun matasa a jihar Zamfara sun gudanar da mummunar zanga-zanga a kan babbar hanyar Gusau - Kaura Namoda da ke jihar

- Matasan dauke da makamai sun mamaye hanyar ne da safiyar ranar Litinin saboda yawan hare-haren da 'yan fashi ke kaiwa a yankunansu

- Sun kuma lalata wasu ababen hawa kafin jami'an tsaro suka zo suka tarwatsa su domin hana cunkoso

Fusatattun matasa dauke da makamai sun yi wata mummunar zanga-zanga a kan babbar hanyar Gusau - Kaura Namoda a jihar Zamfara.

Shaidun gani da ido sun fadawa gidan talabijin na Channels cewa masu zanga-zangar sun mamaye hanyar ne da safiyar ranar Litinin saboda yawan hare-haren da 'yan fashi ke kaiwa a yankunansu.

KU KARANTA KUMA: 'Yan bindiga sun nemi a biya kudin fansa naira Miliyan 50 domin sakin wadanda aka sace a Neja

Matasan Zamfara sun toshe babbar hanya, sun lalata ababen hawa a wata mummunar zanga-zanga da suke gudanarwa
Matasan Zamfara sun toshe babbar hanya, sun lalata ababen hawa a wata mummunar zanga-zanga da suke gudanarwa Hoto: @PremiumTimesng
Asali: UGC

Daya daga cikin matafiyan da suka makale a kan hanyar ya bayyana cewa matasan sun tare babbar hanyar da ke mahadar Kurya inda suka fara lalata motocin jama'a da ke tafiya a kan hanyar.

Jaridar Sahara Reporters ta kuma ruwaito cewa wani ganau ya bayyana cewa, an dakile zirga-zirga a daidai inda barayin ke wucewa don mamaye garuruwan.

Sun yi Allah wadai da rashin tsaro da hare-hare da mutanen yankin suke faman sha a hannun 'yan ta'addan.

Yayin da zanga-zangar ke gudana, an ce jami'an 'yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zangar don tabbatar da kwararar ababen hawa a kan hanya.

Mazauna Zamfara na rayuwa cikin fargaba sakamakon ci gaba da kai hare-hare da 'yan fashi ke yi wa al'ummomi a sassa daban-daban na jihar.

Daya daga cikin hare-haren na baya-bayan nan shi ne kisan sama da mutane 20 lokacin da wasu 'yan bindiga suka afka wa kauyuka biyar a kananan hukumomi biyu na jihar kimanin makonni biyu da suka gabata.

Garuruwan da abin ya shafa sune Gabaken, Rigiya, Donroyi, Torawa, da Riwoji suna cikin ƙananan hukumomin Zurmi da Kaura Namoda na jihar.

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa fusatattun matasa sunyi zanga-zanga kan irin kisan awakin da yan bindiga ke musu a karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-Yanzu: 'Yan Sanda Sun Harbe Sowore Yayin Zanga-Zanga a Abuja

Wannan fushi ya kaisu ga banka wuta a fadar Sarkin Zurmi.

Bidiyon da TVCNews ta samu ya nuna yadda wasu matasa ke kona wasu sashen fadar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel