'Yan bindiga sun nemi a biya kudin fansa naira Miliyan 50 domin sakin wadanda aka sace a Neja
- 'Yan bindiga da suka mamaye yankin Batati da ke karamar hukumar Lavun a jihar Neja, sun nemi a ba su Naira miliyan 50 don mutane biyar da aka sace a lokacin da suka kai wa garin hari
- 'Yan fashin sun yi barazanar ci gaba da rike wadanda abin ya shafa har sai an biya su kudin da suka bukata
- Kimanin ’yan fashi 10 a ranar Juma’a da misalin karfe 8 na dare suka afka wa Batatti suka yi awon gaba da wadanda suka sace tare da raunata wasu da dama
‘Yan bindigar da suka kai hari Batatti a karamar hukumar Lavun da ke jihar Neja sun nemi a ba su kudin fansa na naira miliyan 50 kafin su sako wadanda suka sace.
Wannan ya kasance ne yayinda shugaban majalisar sarakunan gargajiya na jihar Neja kuma Etsu Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar, ya kira taron gaggawa na gundumomi da hakimai kan sace mutane biyar da aka yi a Batatti.
An gano cewa 'yan bindigar sun riga sun bukaci naira miliyan 50 a matsayin kudin fansa don sako mutanen biyar din duk da cewar sun kwashe muhimman kayayyaki da suka hada da kwamfutar tafi-da-gidanka da wayoyin hannu.
KU KARANTA KUMA: Sanata Shehu Sani ya bayyana yadda aka saci mutane rututu a kauyen Neja da rana-tsaka
Jaridar The Nation ta tattaro cewa 'yan bindigar sun yi barazanar ci gaba da rike wadanda lamarin ya rutsa da su har sai an biya su N50 miliyan.
Idan za tuna, ‘yan fashi da yawansu ya kai 10 sun auka wa Batatti a ranar Juma’a da karfe 8:00 na dare, suka yi garkuwa da mutane biyar tare da jikkata wasu da dama.
Wani ganau ya bayyana cewa ‘yan fashin sun yi barna a shagon wani Kolade Olushoshola da ke Batatti da sauran shagunan da ke kan hanyar babban titin Bida-Mokwa, Daily Trust ta ruwaito.
Jawabin ganau din ya nuna cewa wani mai suna Zacharia, wanda ke shagon don siyan katin waya lokacin da 'yan fashin suka kai hari, yana daga cikin wadanda suka samu raunuka.
An tattaro daga majiya mai tushe cewa 'yan fashin sun isa Batatti cikin wata farar mota kirar Hillux kuma suka yi sallar Ishai tare da jama’ar yankin kafin su ka yi harbi a sama.
Abin da ‘yan fashin suka yi, in ji shaidar ya ce, ya sanya masu shagunan, kananan yan kasuwa da ke kusa da yankin barin kayayyakinsu da shagunansu don tsiratar da ransu.
"Bayan wasu awanni suna barna a Batatti, sai suka bar yankin ta hanyar garin Gbangbagi zuwa dajin Fazhi da Kutigi hedkwatar karamar Hukumar Lavun," in ji shaidar.
Ba a samu jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda na jihar (PPRO), SDP Wasiu Abiodun ba a lokacin hada wannan rahoton.
KU KARANTA KUMA: Wata Sabuwa: An Zargi Obasanjo da Shirya Makarkashiyar Kifar Da Gwamnatin Buhari
A wani labarin, mun ji cewa awanni kaɗan bayan sace ɗaliban islamiyya da ba'a san adadin su ba a Tegina ƙaramar hukumar Rafi, Gwamnan Neja, Abubakar Sani Bello, ya tafi ƙasar waje, kamar yadda the nation ta ruwaito.
Legit.ng hausa ta gano cewa gwamna Abubakar sani ya tafi ƙasar wajen ne tare da mai ɗakinsa.
A wani jawabi da sakataren yaɗa labarai na jihar, Mary Noel Berje, ya fitar, yace gwamnan yayi wannan tafiya ne domin nemo hanyoyin da za'a warware matsalolin tsaron da suka addabi jihar.
Asali: Legit.ng