Da dumi-dumi: A Karshe APC Ta Bayyana Cikakken Bayanin Haduwar Atiku da Tinubu a Filin Jirgin Sama na Abuja

Da dumi-dumi: A Karshe APC Ta Bayyana Cikakken Bayanin Haduwar Atiku da Tinubu a Filin Jirgin Sama na Abuja

- Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ta yi wasu karin haske game da ganawa tsakanin Tinubu da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar

- Wasu ‘yan Najeriya sun bayyana ra’ayoyi mabanbanta game da ganawar, suna masu cewa shugabannin biyu na iya nuna sha’awar kafa sabuwar jam’iyya kafin 2023

- A martaninta, APC a ranar Asabar, 29 ga Mayu, ta yi watsi da ikirarin cewa an tsara ganawar shugabannin biyu ne

Biyo bayan ra'ayoyi daban-daban da suka bayyana kan ganawar shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe, Abuja a ranar Juma'a, 28 ga watan Mayu, jam'iyyar mai mulki ta mayar da martani.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa wasu masu amfani da shafin Twitter sun dage cewa taron shugabannin biyu bazai rasa nasaba da takarar shugabancin kasar na 2023 ba.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun kai hari wani ofishin' yan sanda da babbar kotu a Imo

Da dumi-dumi: A Karshe APC Ta Bayyana Cikakken Bayanin anawar Atiku da Tinubu a Filin Jirgin Sama na Abuja
Da dumi-dumi: A Karshe APC Ta Bayyana Cikakken Bayanin anawar Atiku da Tinubu a Filin Jirgin Sama na Abuja Hoto: The Punch
Asali: UGC

Tinubu da Atiku sun yi haduwar bazata ne a Filin jirgin saman Abuja

Da take martani a kan jita-jitar, APC, ta yi magana kai tsaye a ranar Asabar, 29 ga Mayu, ta shafinta na Twitter, @APCUKingdom, cewa Tinubu ya yi haduwar bazata ne da Atiku a filin jirgin sama.

Hakanan jiga-jigan biyu sun isa filin jirgin saman a kusan lokaci guda kuma sun gaisa cikin girmamawa kafin suka ci gaba da tafiyarsu mabanbanta.

A cewar jam’iyyar, gajeren ‘taron’ ba a shirya shi ba, ta kara da cewa Asiwaju Tinubu ba ya cikin ayarin masu tarbar tsohon mataimakin shugaban kasar zuwa gida Najeriya.

Rubutun ya zo kamar haka:

"Wani sakon da Reno Omokri @renoomokri ya wallafa a shafinsa na Twitter da karfe 6:24 na safe a ranar 29 ga Mayu, 2021, wanda aka yiwa bidiyon take da:" Tinubu Ya Tarbi @atiku a filin jirgin sama yayinda tsohon mataimakin shugaban kasar ya dawo Najeriya ".
"Wannan shi ne don sanar da jama'a cewa bayanan da ke kunshe a cikin rubutun da aka ambata a sama karya ne, kuskure ne, kuma shiryayye ne daga masu yada labaran karya don yaudarar 'yan Najeriya, neman suna da kuma samun karramawa da bai dace ba."
"Mai girma, tsohon gwamnan jihar Legas kuma jagoran jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar sun hadu a daren jiya, 28 ga Mayu, 2021 a filin jirgin saman ba zato ba tsammani!"

KU KARANTA KUMA: Gwamnan Najeriya Ya Koka, Ya Bayyana Abinda Sojoji Ke Bukata Don Kawo Karshen Rashin Tsaro A Jihar Zamfara

Dole ne yan Najeriya suyi watsi da ikirarin Reno Omokri

Jam’iyyar ta kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da su yi watsi da abin da ta kira karami da wallafar neman suna wanda Reno Omokri ya kirkira.

Ta kara da cewa:

"Muna rokon 'yan Najeriya da su yi watsi da kananan maganganu, da kuma wallafar neman suna da Reno Omokri wanda aka fi sani da Wendell Smith yayi Na gode."

A baya mun ji cewa, 'Yan Najeriya sun bayyana ra'ayoyi mabanbanta game da bayyanar hotunan shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, lokacin da ya karbi bakuncin jigon jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe, Abuja.

Legit.ng ta rahoto cewa Jaridar The Punch da ta buga hotunan bata bayyana lokacin da aka dauke su ba.

An tattaro cewa Tinubu, ya yiwa Atiku, wanda shine tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa na PDP a lokacin babban zaben 2019, maraba da dawowa gida Najeriya da yammacin ranar Juma’a, 28 ga Mayu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel