Gwamnan Najeriya Ya Koka, Ya Bayyana Abinda Sojoji Ke Bukata Don Kawo Karshen Rashin Tsaro A Jihar Zamfara
- Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, ya ce wasu runduna na matukar dagula kokarinsa na kawo karshen ta'addancin a jihar
- Matawalle wanda ya bayyana hakan a ranar Asabar, 29 ga watan Mayu, ya ce jihar na bukatar karin sojoji domin kawo karshen kalubalen rashin tsaro da ke hauhawa
- A cewarsa, rashin daukar matakan gaggawa daga jami'an tsaro a hare-haren da 'yan bindiga ke kaiwa a jihar na daga cikin abunda ke kawo cikas ga nasarar da ake samu a yakin
Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya danganta yawaitar ayyukan 'yan ta'adda a jihar da rashin daukar matakan gaggawa daga jami'an tsaro.
Jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito cewa gwamnan ya kara da cewa jihar na bukatar karin dakaru domin tunkarar kalubalen tsaro a yanzu.
KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun sake kai hari garuruwan Neja, sun kashe mutane da dama
Legit.ng ta tattaro cewa wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba Matawalle shawara na musamman kan harkokin yada labarai da sadarwa, Zailani Bappa ya fitar a ranar Asabar, 29 ga watan Mayu.
Matawalle ya lura cewa ya zama wajibi ga gwamnati ta yi bayani game da hauhawan hare-hare a cikin 'yan kwanakin nan.
A cewarsa, lokacin da ya hau mulki, ya yi nazarin matsalolin tsaro da ke addabar jihar kuma ya yi amannar cewa babbar hanyar magance su ita ce ta hanyar tattaunawa.
KU KARANTA KUMA: 2023: Hotuna Sun Nuna Yadda Tinubu Ya Tarbi Atiku a Filin Jirgin Sama Yayinda Ya Dawo Daga Dubai
Ya kara da cewa an yi amfani da dukkanin dabaru, yana mai cewa addu'oin da suke yi shine na ganin cewa lamarin ya samu gagarumar nasara.
Sanarwar ta ce:
“Daya daga cikin matsalolin da ke hana nasarar yaki da‘ yan fashi a cikin jihar shi ne rashin daukar matakan gaggawa daga jami’an tsaro a hare-haren ‘yan fashi. Don haka, an umarci dukkan kwamandojin da aka tura a jihar da su dauki matakan da suka dace wadanda za su tabbatar da matakan gaggawa kan lamarin.
“Gwamnati tana sane da irin kalubalen da ke tattare da dokokin tsaro musamman da yake da alama sun wuce gona da iri. Duk da wannan karancin su, Gwamnati ta nemi a ba jihar ta Zamfara kulawa ta musamman dangane da tura karin dakaru don hanzarta magance duk wata barazanar tsaro.”
Jaridar Vanguard ta kuma ruwaito cewa, Matawalle, ya yaba da yadda sojoji da sauran jami'an tsaro ke gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
Ya bayyana cewa gwamnati da mutanen kirki na jihar za su yi godiya tare da nuna godiya ga Shugaba Muhammadu Buhari saboda damuwa da goyon baya da yake nunawa kan halin da 'yan kasa ke ciki a ci gaba da yaki da 'yan fashi da sauran laifuka.
A wani labarin, fusatattun matasa sunyi zanga-zanga kan irinsu kisan awakin da yan bindiga ke musu a karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara.
Wannan fushi ya kaisu ga banka wuta fadar Sarkin Zurmi.
Bidiyon da TVCNews ta samu ya nuna yana wasu matasa ke kona wasu sashen fadar.
Asali: Legit.ng