Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun kai hari wani ofishin' yan sanda da babbar kotu a Imo

Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun kai hari wani ofishin' yan sanda da babbar kotu a Imo

- Wasu ‘yan bindiga a ranar Asabar, 29 ga watan Mayu, sun afkawa karamar hukumar Njaba inda suka kone ofishin ‘yan sanda a jihar Imo

- A cewar rahoton, wadanda ake zargin 'yan bindigar ne sun kuma kona kotun Majistare ta Atta da kuma babbar kotu sannan suka lalata kayayyaki a jihar

- Yarima mai jiran gado na yankin, Remigiius Azike, ya ruwaito cewa lamarin ya faru ne lokacin da mutanen kauyen ke bacci

Wasu ‘yan bindiga a ranar Asabar sun kona hedikwatar rundunar’ yan sanda ta Atta da ke Karamar Hukumar Njaba ta Jihar Imo.

'Yan daban sun kuma kona Kotun Majistare ta Atta da Babbar Kotu sannan kuma suka lalata cibiyar kiwon lafiyar garin.

KU KARANTA KUMA: Hatsarin jirgin soji: NAF ta bayyana dalilin da yasa aka kyale kananan matuka suna jigila da COAS da sauransu

Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun kai hari wani ofishin' yan sanda da babbar kotu a Imo
Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun kai hari wani ofishin' yan sanda da babbar kotu a Imo Hoto: @Govhopeuzodinma
Asali: Twitter

Wannan lamarin ya haifar da matukar damuwa a yankin, domin kuwa matasan garin sun kusa kashe wakilin jaridar Punch wanda ya ziyarci yankin a safiyar ranar Asabar.

An kwace kayan aikinsa, aka lalata su sannan kuma aka karɓe masa kuɗi.

An kona ginin ne tsakanin karfe 1:00 zuwa 2:00 na tsakar dare.

Majiyoyin garin sun shaida cewa maharan sun yi ta harbe-harbe har na kusan awa daya kafin su taba gine-ginen gwamnati da ke yankin.

Yarima mai jiran gado na yankin, Remigiius Azike, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne lokacin da mazauna kauyen suka kwanta.

Wani tsohon babban shugaban yankin, John Agbaso, ya shaida wa jaridar cewa garin na cikin radadi.

Ya ce mako guda kenan da wasu mutane da ba a san ko su wanene ba suka cinna wa gidan shugaban garin, Chijioke Duruonyeokwu wuta tare da kashe matarsa.

Da yake kira ga gwamnati da ta kawo musu dauki, shugaban garin ya ce rashin tsaro na ci gaba da karuwa a yankin.

Lokacin da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Bala Elkana, ya ce ba a sanar da shi ba.

Tsagerun yan bindiga sun kuma afkawa ofishin yan sanda, sun kashe jami'ai 3

A wani lamari makamancin haka, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Jami'an yan sanda uku na ofishin Umutu dake karamar hukumar Ukwani a jihar Delta sun rasa rayukansu cikin daren Juma'a, 28 ga watan Mayu, 2021.

KU KARANTA KUMA: Gwamnan Najeriya Ya Koka, Ya Bayyana Abinda Sojoji Ke Bukata Don Kawo Karshen Rashin Tsaro A Jihar Zamfara

Hakan ya biyo bayan harin da wasu yan bindiga suka kai ofishin yan sandan misalin karfe 1:30 na dare.

A cewar rahoton TVCNews, Kakakin hukumar yan sandan jihar, Edafe Bright, ya ce yan bindigan sun budewa yan sandan wuta inda suka hallaka uku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng