2023: Hotuna Sun Nuna Yadda Tinubu Ya Tarbi Atiku a Filin Jirgin Sama Yayinda Ya Dawo Daga Dubai

2023: Hotuna Sun Nuna Yadda Tinubu Ya Tarbi Atiku a Filin Jirgin Sama Yayinda Ya Dawo Daga Dubai

- Yan Najeriya sun yi cece kuce kan tarbar da Tinubu yayi wa Atiku a filin jirgin sama na Abuja

- Atiku, wanda ya kasance dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a yayin babban zaben shekarar 2019, ya iso Najeriya ne a ranar Juma'a, 28 ga Mayu

- Tinubu, wanda aka ce yana hararar kujerar da ta fi kowacce a kasar nan, ba lallai ne ya samu goyon bayan wasu gwamnoni da aka zaba a karkashin APC ba

'Yan Najeriya sun bayyana ra'ayoyi mabanbanta game da bayyanar hotunan shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, lokacin da ya karbi bakuncin jigon jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe, Abuja.

Legit.ng ta rahoto cewa Jaridar The Punch da ta buga hotunan bata bayyana lokacin da aka dauke su ba.

KU KARANTA KUMA: Hatsarin jirgin soji: NAF ta bayyana dalilin da yasa aka kyale kananan matuka suna jigila da COAS da sauransu

2023: Hotuna Sun Nuna Yadda Tinubu Ya Tarbi Atiku a Filin Jirgin Sama Yayinda Ya Dawo Daga Dubai
2023: Hotuna Sun Nuna Yadda Tinubu Ya Tarbi Atiku a Filin Jirgin Sama Yayinda Ya Dawo Daga Dubai Hoto: The Punch
Asali: UGC

An tattaro cewa Tinubu, ya yiwa Atiku, wanda shine tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa na PDP a lokacin babban zaben 2019, maraba da dawowa gida Najeriya da yammacin ranar Juma’a, 28 ga Mayu.

A bisa ga hotunan, dukkan shugabannin sun rungume juna sannan kuma suka yi gaisuwa cikin raha.

Atiku da Tinubu sun kasance abokai na kwarai kuma dukansu sun kasance mambobin jam'iyyar APC har zuwa lokacin da tsohon mataimakin shugaban kasar ya sauya sheka zuwa jam'iyyar adawa ta PDP domin cimma burin zama shugaban kasa.

A halin da ake ciki, ‘yan Najeriya sun mayar da martani game da shirin da ake zargin Tinubu da Atiku sun kulla gabanin babban zaben na 2023 kamar yadda ake ganin jam’iyyar APC na nuna burin ta na ganin ta gaji Shugaba Buhari a 2023.

@njoku_ije

'Yan Najeriya suna son zabar mazajen da ke fama da rashin lafiya a kan karagar mulki. Me yasa ba zamu gwada matasa ba?

@mrshinger ya ce:

Ina dandalin matasa. har yanzu matasa basu shirya fara wani abu ba ... lokaci yana tafiya kuma babu wani shugaba ko guda daya babu mataimaki. Muna da kudaden daukar nauyin kowa. kada matashin da ya zabi APC ko pdp.

@CountLuchino ya yi martani:

Yayinda mutane suke jayayyar siyasa a cikin rukuninsu da wuraren shan giya ba tare da tunani mai ma’ana ba, manyan 'yan wasan suna hadewa da daidaitawa a bayan fage.

@PattersonGolde

Wata kila Tinubu yana aiki don darewa matsayin Mataimakin Shugaban kasa saboda ya san cewa ba shi da damar zama Shugaban kasa.

Nan da shekara 2, har yan adawa sai sun jinjinawa shugaba Buhari: Fadar Shugaban kasa

A wani labarin kuma, fadar shugaban kasa, a ranar Juma'a, ta bayyana cewa kafin karewar wa'adin shugaba Muhammadu Buhari a 2023, ko masu adawa sai sun jinjinawa masa.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya bayyana hakan a jawabin murnar cikar Buhari shekaru 6 kan mulki.

KU KARANTA KUMA: Jam'iyar APC ta dakatar da Hon. Muhammad Gudaji Kazaure

Adesina ya lissafa jerin nasarori da ayyukan da shugaba Muhammadu Buhari yayi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel