Rundunar Yan Sanda Ta Sheƙe Yan Bindiga 5, Ta Damƙe 16 a Jihar Katsina

Rundunar Yan Sanda Ta Sheƙe Yan Bindiga 5, Ta Damƙe 16 a Jihar Katsina

- Rundunar yan sanda a jihar Katsina ta samun nasarar sheke yan bindiga biyar tare da damƙe wasu 16 a musayar wuta

- Rundunar tace ta samu waɗan nan nasarori ne a wasu kananan hukumomi dake ƙarƙashin jihar ta Katsina

- Kakakin rundunar na jihar, SP Gambo isa, shine ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar ranar Laraba

Rundunar yan sanda ta aike da yan bindiga biyar lahira, ta samu nasarar cafke wasu 16 tare da kwato shanun da suka sace a jihar Katsina, kamar yadda the nation ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Daga Ƙarshe, FG Ta Faɗi Matsayarta Kan Kudirin Soke Bautar Ƙasa NYSC

Yan sandan sun kuma kwato wani adadi na miyagun ƙwayoyi daga hannun yan bindigan, kamar yadda Guardian ta ruwaito.

Kakakin hukumar yan sanda na jihar Katsina, SP Gambo Isa, shine ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar ranar Laraba.

Rundunar Yan Sanda Ta Sheƙe Yan Bindiga 5, Ta Damƙe 16 a Jihar Katsina
Rundunar Yan Sanda Ta Sheƙe Yan Bindiga 5, Ta Damƙe 16 a Jihar Katsina Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Isah yace an kama yan bindigan ne lokacin da sukayi artabu tsakanin yan sanda da yan bindigan a wasu daga cikin ƙananan hukumomin jihar.

Isah yace: "Jami'an yan sanda sun kashe yan bindiga biyar lokacin da suka yi musayar wuta a ƙananan hukumomin Kafur, Ɗanja, Ɗutsin-ma, Safana, Batsari da kuma Maƙera a Funtua."

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Yan Bindiga Sun Hallaka Wani Ɗan Sanda, Sun Bankawa Motar Sintiri Wuta

"Jami'an sun kuma samu nasarar cafke wasu guda 15 a fafatawar da suka yi, Yayin da suka damƙe wani mai suna Musa Shamsuddin, da zargin yana zuwa cikin jeji duba lafiyar yan bindigan da suka ji rauni."

"An ƙwato bindigun gargajiya da kuma wani adadi na alburusai a hannun yan bindigan.

A wani labarin kuma Shugaba Buhari Baya Sha'awar Zarcewa a Kan Karagar Mulki, Inji Garba Shehu

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari baya sha'awar zarcewa akan mulkin Najeriya zango na uku kamar yadda ake jita-jita

Kakakin shugaban ƙasa, Malam Garba Shehu, shine ya bayyana haka a wata fira da yayi da gidan talabishin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel