Shugaba Buhari Baya Sha'awar Zarcewa a Kan Karagar Mulki, Inji Garba Shehu

Shugaba Buhari Baya Sha'awar Zarcewa a Kan Karagar Mulki, Inji Garba Shehu

- Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari baya sha'awar zarcewa akan mulkin Najeriya zango na uku kamar yadda ake jita-jita

- Kakakin shugaban ƙasa, Malam Garba Shehu, shine ya bayyana haka a wata fira da yayi da gidan talabishin

- Yace shugaban yana matuƙar damuwa da hare-haren da ake kaiwa ofisoshin hukumar zaɓe INEC a sassa daban-daban na ƙasar nan

Kakakin shugaban ƙasa, Malam Garba Shehu, yace shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ba zai nemi zarcewa zango na uku a cikin ofis ba, kuma baya sha'awar yin hakan.

KARANTA ANAN: Mako Ɗaya Bayan Mutuwar COAS Ibrahim Attahiru, Rundunar Soji Ta Shirya Gagarumin Bikin POP

A cewar Mr, shehu, wanda ya tattauna da gidan talabishin na Arise tv ranar Talata, Shugaban ƙasa yana matuƙar damuwa kan hare-haren da ake kaiwa ofisoshin INEC da caji ofis ɗin yan sanda kuma a ƙona su a sassa daban-daban na ƙasar nan.

Shugaban ya bayyana masu hannu a waɗannan hare-haren a matsayin masu son kawo tashin-tashina.

Shugaba Buhari Baya Sha'awar Zarcewa a Kan Karagar Mulki, Inji Garba Shehu
Shugaba Buhari Baya Sha'awar Zarcewa a Kan Karagar Mulki, Inji Garba Shehu Hoto: @aminiyatrust
Asali: Twitter

Hakanan kuma kakakin shugaban ƙasan, Malam Shehu, ya musanta zargin da wasu keyi cewa hare-haren da ake kaiwa ofisoshin hukumar zaɓe INEC wani ƙoƙari ne na hana zaɓen 2023.

KARANTA ANAN: Rundunar Yan Sanda Ta Yi Ram da Jami’in Soji Kan Kashe Wani Hamshaƙin Ɗan Kasuwa

Wanda idan hakan ta faru shugaban ƙasa zai cigaba da zama kan madafun iko har sai komai ya dai-daita.

Malam Shehu yace: "Na yarda cewa, abun tashin hankali ne yadda ake kaiwa ofisoshin INEC da caji ofis ɗin yan sanda hari wanda wasu marasa kishin ƙasa, masu son kawo tashin-tashina suke ɗaukar nauyi."

"Hukumomin tsaro zasu ɗauki mataki akan lamarin. Shugaba Buhari bashi da hannu kan wannan hare-haren kuma bashi da sha'awar komawa zango na uku, saboda haka za'a yi zaɓe a 2023."

Yan Najeriya da dama sun tofa albarkacin bakinsu kan wannan magana. Legit.ng hausa ta tattaro muku wasu daga cikin ra'ayoyin jama'a.

Umar Abubakar:

"in babu abu me ya kawo shi? kada kace min har kun fara gutsura masa wannan maganar,tunda kace haka to nasan kishiyar hakan kuke nufi, ba zanyi mamaki ba in kuka fito 2022 kuka fara neman zaben Buhari a zango na uku"

Lawan Inuwa:

"Don Allah ku bashi shawara ya kara neman zarcewa karo na uku domin ya iya mulki sosai"

Balkisu Tahiru Ibrahim:

"Ko yayi sha'awa ina zai samu dan kuwa dan Nigeria ya dandana kudarsa, sunan littafin buhariya jiki magayi"

A wani labarin kuma Bayan Mutuwar COAS Attahiru, FG Ta Bayyana Ranar da Wasu Sabbin Jirgaen Yaƙi Zasu Iso Najeriya

Gwamnan CBN ya bayyana cewa nan da yan watanni jiragen yaƙi 6 zasu iso Najeriya daga ƙasar Amurka.

Gwamnan yace wannan na daga cikin jirage 12 da gwamnatin tarayya tayi yarjejeniya da Amurka shekara uku da suka gabata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262