Daga Ƙarshe, FG Ta Faɗi Matsayarta Kan Kudirin Soke Bautar Ƙasa NYSC
- Gwamnatin tarayya ta bayyana matsayarta kan rahoton dake nuna cewa za'a soke shirin bautar ƙasa na matasa NYSC
- Ministan Matasa da wasanni, Sunday Dare, a wani rubutu da yayi a shafinsa na tuwita, ya musanta rahoton
- Yace gwamnati zata cigaba da garambawul a shirin, kuma Najeriya na tare da matasanta
Ministan matasa da wasanni, Sunday Dare, yayi watsi da rahoton dake nuna cewa za'a soke shirin bautar ƙasa da matasa ke yi bayan kammala karatu, NYSC.
KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Yan Bindiga Sun Hallaka Wani Ɗan Sanda, Sun Bankawa Motar Sintiri Wuta
Kwanaki kaɗan da suka shuɗe, an yaɗa jita-jitar cewa za'a soke shirin bautar ƙasa na tsawon shekara ɗaya da matasa ke yi biyo bayan tsallake karatu na biyu da kudirin yayi a majalisar wakilan ƙasar nan.
Kudirin dai na gaban yan majalisar wakilan ƙasar nan, wanda yake buƙatar majalisar ta soke shirin sabida wasu na kallonshi a mara amfani.
Da yake maida martani kan rahoton a shafinsa na dandalim sada zumunta Tuwita, Ministan yace gwamnatin tarayya zata cigaba da gudanar da shirin.
KARANTA ANAN: Mako Ɗaya Bayan Mutuwar COAS Ibrahim Attahiru, Rundunar Soji Ta Shirya Gagarumin Bikin POP
Ministan yace:
"Shirin bautar ƙasa NYSC na ɗaya daga cikin abinda muka riƙe wajen kawo cigaba ga matasan ƙasar nan. Gwamnatin tarayya zata cigaba da gudanar dashi da kuma ƙoƙarin ƙara inganta shi."
"Cigaba da garambawul a tsarin na bautar ƙasa yana nan, Najeriya na tare da matasan ta."
Legit.ng hausa ta tattaro muku wasu daga cikin ra'ayoyin yan Najeriya game da wnnan kudiri.
Aisha Usman:
"Alhamdulillah Masha Allah inda Rai dai semunsa kayan N Y S C Allah yanuna ma duk mai buri."
Real Abdul Tmw:
"Da hannun mu muke zaban makiya cigabanmu Sanatoci da yan majalisu Allah ya mana maganin ku."
Abdul Aziiz Lawal:
"Allah Dai Ya Biya! Nan Kam Baba Ya Kyauta Muna Wallah"
A wani labarin kuma Rundunar Yan Sanda Ta Yi Ram da Jami’in Soji Kan Kashe Wani Hamshaƙin Ɗan Kasuwa
Jami'an hukumar yan sanda sun yi ram da wani jami'in soji da ake zarginsa da kashe ɗan kasuwa a ƙaramar hukumar Ikot Abasi.
Mai motar da aka kashe ya ɗauki sojan ne domin ya rage masa hanya ba tare da sanin kashe shi zai yi ba.
Asali: Legit.ng