Da Ɗumi-Ɗumi: Yan Bindiga Sun Hallaka Wani Ɗan Sanda, Sun Bankawa Motar Sintiri Wuta a Wani Sabon Hari a Delta
- Wasu yan bindiga sun hallaka ɗan sanda guda ɗaya, sun ƙona motar sintirin yan sanda a jihar Delta
- Kakakin hukumar yan sanda na jihar, Edafe Bright, ya tabbatar da kai harin, amma yace har yanzun suna gudanar da bincike
- Yace an kai wa jami'an yan sanda hari a ƙauyen Akwukwu Igbo, amma an samu nasarar damƙe shugaban maharan
An hallaka wani ɗan sanda ɗaya tare da ƙona motar sintiri a wani sabon hari da yan bindiga suka kai ƙaramar hukumar Aniocha dake jihar Delta, kamar yadda Punch ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Shugaba Buhari Baya Sha'awar Zarcewa a Kan Karagar Mulki, Inji Garba Shehu
Kakakin hukumar yan sandan jihar, Edafe Bright, ya tabbatar wa dailytrust da faruwar lamarin, amma yace an kama wasu daga cikin maharan.
Yace: "Eh, an kaiwa jami'an mu hari da misalin ƙarfe 6:20 na safiyar yau Laraba a ƙauyen Akwukwu Igbo. Ɗaya daga cikin jami'an mu ya rasa ransa sannan sun ƙona motar sintiri."
"Amma mun samu nasarar damƙe shugaban waɗanda suka kawo harin, a halin yanzun muna cigaba da bincike."
Edafe ya ƙara bayyana cewa rundunar yan sanda na cigaba da ƙoƙari domin ganin an kamo sauran mutanen da suka gudu.
KARANTA ANAN: Rundunar Yan Sanda Ta Sheƙe Yan Bindiga 5, Ta Damƙe 16 a Jihar Katsina
Ana cigaba da samun ƙaruwar kai hare-hare ga jami'an hukumar yan sanda a yankin kudancin ƙasar nan.
A wani labarin kuma Daga Ƙarshe, FG Ta Faɗi Matsayarta Kan Kudirin Soke Bautar Ƙasa NYSC
Ministan matasa da wasanni, Sunday Dare, yayi watsi da rahoton dake nuna cewa za'a soke shirin bautar ƙasa da matasa ke yi bayan kammala karatu, NYSC.
Kwanaki kaɗan da suka shuɗe, an yaɗa jita-jitar cewa za'a soke shirin bautar ƙasa na tsawon shekara ɗaya da matasa ke yi biyo bayan tsallake karatu na biyu da kudirin yayi a majalisar wakilan ƙasar nan.
Asali: Legit.ng