Yanzu-yanzu: Gwamna El-Rufai ya tsige masu mukaman siyasa 19

Yanzu-yanzu: Gwamna El-Rufai ya tsige masu mukaman siyasa 19

- Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, ya amince da sallamar wasu mutum 19 da ke rike da mukaman siyasa

- Hakan na daga cikin kokarin da gwamnatin jihar ke yi na rage yawan ma’aikata

- Lamarin ya shafi masu ba da shawara na musamman guda biyu, Mataimakin Shugaban Ma’aikata da kuma mataimaka na musamman da dama

Daga cikin shirin rage yawan ma'aikata da gwamnatin jihar Kaduna ke yi, Gwamna Nasir El-Rufai ya amince da sallamar wasu masu rike da mukaman siyasa guda 19.

Gwamnan ya ce ma'aikata 19 da aka sallama din su ne kashin farko na ma'aikatan gwamnati da za su bar aikin gwamnati, a kokarin kawo sauyi a bangaren ma’aikata.

Wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar a Twitter a ranar Laraba, 26 ga watan Mayu, ta ce jami’an da abin ya shafa sun hada da masu ba da shawara na musamman guda biyu, Mataimakin Shugaban Ma’aikata da kuma mataimaka na musamman da dama.

Yanzu-yanzu: Gwamna El-Rufai ya tsige masu mukaman siyasa 19
Yanzu-yanzu: Gwamna El-Rufai ya tsige masu mukaman siyasa 19 Hoto: @elrufai
Asali: Facebook

KU KARANTA KUMA: Anyi cece-kuce yayinda da wani mutumi ya budewa hadimi kofar mota kafin na Gwamna a cikin wani bidiyo

“Malam Nasir El-Rufai ya godewa jami’an da aka sallama daga aiki kan hidimar da suka yi wa jihar tare da yi musu fatan alheri a ayyukan da za su yi nan gaba,” in ji sanarwar.

A cewar sanarwar, Bala Yunusa Mohammed, mataimakin shugaban ma’aikatan majalisar dokoki (DCOSL), Halima Musa Nagogo, mataimakiya ta musamman ga DCOSL da Umar Abubakar, wani mataimaki na musamman ga DCOSL, na daga cikin wadanda lamarin ya shafa.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, Ben Kure, mai ba da shawara na musamman kan harkokin siyasa, Mustapha Lynda Nyusha da Jamilu Gwarzala Dan Mutum, mataimaka na musamman ga mai ba da shawara na musamman kan harkokin siyasa su ma za su fice daga aikin, ciki har da Umar Haruna, mataimaki na musamman kan harkokin siyasa.

Sai kuma mai ba da shawara na musamman kan ci gaban zamantakewar al'umma, Zainab Shehu, mataimaki na musamman ga mai ba da shawara na musamman, Stephen Hezron da Mohammed Bello Shuaibu, babban mataimaki kan harkokin masu ruwa da tsaki, da kuma babban mataimaki na musamman kan matasa Aliyu Haruna.

Har ila yau abun ya shafi Halima Idris, mataimakiya ta musamman kan fasahar kere-kere, Engr Aliyu Alhaji Salihu, Darakta Janar na Hukumar Sayen Kayan Gwamnati, Mataimaki na Musamman kan Hulda da Jama’a Ashiru Zuntu da Saida Sa’ad, babbar Mataimakiya ta Musamman.

KU KARANTA KUMA: Mutumin da ya kai wa Limamin Harami hari ya ce shi ne Mahdi

A cewar sanarwar, mataimaki na musamman kan shirye-shirye Elias Yahaya da mataimaki na musamman ga sakataren gwamnatin jihar Kaduna, Tasiu Suleiman Yakaii, suna cikin jerin wadanda aka sallama.

Haka kuma mataimaki na musamman kan harkokin tattalin arziki, Samuel Hadwayah da Ahmed Mohammed Gero, babban mataimaki na musamman kan harkokin muhalli sun shiga.

Legit.ng ta zakulo wasu daga cikin martanin jama'a:

@NaseerIsah_ ya ce:

“Wannan shine yadda za a ragge tsadar gwamnati ina fatan sauran gwamnoni da shugaban kasa za su dau tsarin.”

@arewaboi_212 ya yi martani:

"Hakanan ku rage alawus din yan majalisa, motoci da yawa suna tafiya babu komai a cikin jerin gwanon motoci, wadancan miliyoyin kudin da suke kashewa a motoci, ina jin hakan shima yana bukatar a duba.”

@AlbarkaTemi3

"Duk wannan S.A din na kan yi mamakin menene aikinsu, da gaske mallam a wannan karon kana kan hanya. Da yawa ba za su so ba amma yana da alkiblar mai kyau idan har za mu ciyar da tattalin arzikin jihar Kaduna zuwa mataki na gaba. Na gode.”

A wani labarin, babbar jam`iyyar adawa ta PDP ta zargi gwamnatin jihar Kaduna karkashin Mallam Nasiru El-Rufai da jefa makomar al`ummar jihar cikin hadari ta hanyar cin bashin da zai iya zama barazana ga al`ummomi masu tasowa.

Jam`iyyar PDP ta ce a cikin shekaru shida da suka wuce, gwamnatin APC mai mulki a jihar ta ci bashin da ya kai N170bn, kuma babu wani abin a zo a gani na wannan kudin.

PDP dai ta yi zargin cewa babu ranar biyan bashin amma tuni jam`iyyar APC ta musanta zargin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel