Anyi cece-kuce yayinda da wani mutumi ya budewa hadimi kofar mota kafin na Gwamna a cikin wani bidiyo

Anyi cece-kuce yayinda da wani mutumi ya budewa hadimi kofar mota kafin na Gwamna a cikin wani bidiyo

- Wani mutum ya wallafa wani faifan bidiyo mai ban sha'awa wanda ya shafi wani gwamnan jiha na Najeriya da daya daga cikin hadimansa

- A cikin bidiyon, wani mutumi da ake ganin mataimakin hadiminsa ne ya zo ya bude masa kofar mota

- Abin mamakin shine, bayan an bude wa hadimin mota ya fito sai shima ya ya je ya bude kofar motar gwamnan

'Yan Najeriya sun yi martani a kan wani bidiyo da ke yawo wanda ya hasko dan dirama da ya wakana tsakanin wani gwamna da daya daga cikin hadimansa wanda mutane basu saba gani ba.

A cikin bidiyon wanda ya yadu a shafin Twitter, motar gwamnan jihar Kaduna Nair El-Rufai ta tsaya a wani wurin da ba a bayyana ba.

KU KARANTA KUMA: Kudu ta hadewa arewa kai - Kungiyar Dattawan Arewa sun koka, sun zargi Buhari

Anyi cece-kuce yayinda da wani mutumi ya budewa hadimi kofar mota kafin na Gwamna a cikin wani bidiyo
Anyi cece-kuce yayinda da wani mutumi ya budewa hadimi kofar mota kafin na Gwamna a cikin wani bidiyo Hoto: @AliyuUthman
Asali: Twitter

A cikin faifan bidiyon da @AliyuUthman ya wallafa, wani mutumi ya fito daga kujerar direba domin bude wa wani hadimin Gwamnan kofar kujerar fasinja ta gaba.

Abun shaawa kuma cikin sauri, sai hadimin ya bude kofar motar kujerar baya sannan sai ga gwamnan jihar Kaduna ya fito.

KU KARANTA KUMA: Shugaban kasar Libya ya kawowa shugaba Buhari ziyara Aso Villa

Wasu 'yan Najeriyar sun nuna fushinsu a kan abin da suka bayyana a matsayin maimaicin ayyuka da aka nuna a bidiyon. Sai dai wasu da dama ba su ga laifi a cikin hakan ba.

@Detolanny ya ce:

"Toh yanzu idan wani ya tambayi mutumin da ke sanye da kwat aikin da yake yi; amsar da zai bayar ita ce" Ni ne mai bude wa wanda ke bude wa gwamna kofa.

"Chai, wannan rayuwar ba ta da daidaito ko kadan."

@GodsgreatG ya yi martani:

"Abin dariya ne sosai yadda muke nuna ra'ayi game da aikin mutane. Muna yi wa aikin su ba’a, aikin da dashi ne suke samun na kaiwa bakin salati.

" Wannan mutumin yana alfahari da aikin sa. Koda ace yana budewa wani da ke bude wa gwamna kofa ne. A halin yanzu muna ta turo shirme da datar 50Mb."

@bekexjj ya ce:

"Ba batun izgili da aikin wani ba ne. Maimaicin ayyukan ne. Muna korafi kan barnatar da kudaden gwamnati ne kuma wannan babban misali ne. Mataimaki ga mataimaki ga mataimaki zuwa ga mataimaki."

A wani labarin, babbar jam`iyyar adawa ta PDP ta zargi gwamnatin jihar Kaduna karkashin Mallam Nasiru El-Rufai da jefa makomar al`ummar jihar cikin hadari ta hanyar cin bashin da zai iya zama barazana ga al`ummomi masu tasowa.

Jam`iyyar PDP ta ce a cikin shekaru shida da suka wuce, gwamnatin APC mai mulki a jihar ta ci bashin da ya kai N170bn, kuma babu wani abin a zo a gani na wannan kudin.

PDP dai ta yi zargin cewa babu ranar biyan bashin amma tuni jam`iyyar APC ta musanta zargin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel