Mijina ya yi mafarkin haɗarin kwana ɗaya kafin afkuwarsa – Matar matukin jirgin sojin da yayi haɗari

Mijina ya yi mafarkin haɗarin kwana ɗaya kafin afkuwarsa – Matar matukin jirgin sojin da yayi haɗari

- Matar matukin jirgin da yayi mummunar hatsarin da ya kashe wasu jami’an soji 11, ciki har da Babban hafsan sojan kasa ta magantu

- Jennifer Olufade ta bayyana cewa ana gobe mummunan al'amarin zai afku, mijinta ya yi mafarkin cewa sun yi hatsarin jirgin sama

- Ta bayyana cewa ya farka daga mafarkin a razane sannan ya sanar da ita cewa yaga abun kamar a zahiri

Jennifer Olufade, matar Flt Lt Alfred Olufade, matukin jirgin da yayi mummunar hatsarin da ya kashe wasu jami’an soji 11, ciki har da Babban hafsan sojan kasa, Laftanar Janar Ibrahim Attahiru, a Kaduna ranar Juma’a, ta ce marigayin ya yi mafarkin hadarin kwana daya kafin afkuwarsa.

Jennifer, wacce ta auri marigayi matukin jirgin watanni uku da suka gabata, ta bayyana hakan ne a cikin wasikar alhinin rashin mijin nata wanda ta wallafa a shafinta na Instagram, @joba_star, ranar Litinin.

KU KARANTA KUMA: Magidanci ya tattara kayansa ya bar gida, ya ce matarsa na yawan dukansa, bidiyon ya haddasa cece-kuce

Mijina ya yi mafarkin haɗarin kwana ɗaya kafin afkuwarsa – Matar matukin jirgin sojin da yayi haɗari
Mijina ya yi mafarkin haɗarin kwana ɗaya kafin afkuwarsa – Matar matukin jirgin sojin da yayi haɗari Hoto: @Okeydegeneral
Asali: Twitter

Ta ce ta yi addu'a tare da mijin nata a lokacin da ya farka sannan kuma ya labarta mata mummunan mafarkin.

Ta kara da cewa bayan mafarkin, mijinta ya yi tafiye-tafiye cikin nasara zuwa Enugu da Owerri sannan ya dawo Abuja.

Jennifer ta ce lokacin da ta samu sako daga gare shi cewa za su sake zuwa Kaduna, ta yi kokarin kiran shi a waya don ta hana shi tafiyan amma ba ta samu nasara ba.

KU KARANTA KUMA: Bakin ciki da tashin hankali a Benuwe yayin da Makiyaya suka kashe Manoma sama da 100 a garuruwa 4

Ta rubuta

“Oh walkiya, ka bar ni da wuri. Oh, babban abokina, daga ina zan fara? Na karaya, zuciyata na zafi. Wannan ba abin da ka mini alkawari ba ne; kace zaka kasance a tare dani a koyaushe.

"A ranar 20 ga watan Mayu, da misalin karfe 4:00 na asuba, sai ka tashe ni cike da tsoro ka ce 'baby, baby, na yi mummunan mafarki. Na yi mafarki na yi hatsari a kan hanyata ta zuwa Kaduna.’ Ka ce abin ya zo kamar gaske. Na yi maka addu'a sosai a wannan safiyar kuma na nemi da kada ka damu sannan na tambaye ka manufarka da kuma wanda kuka yi tafiyan tare sai ka ce mani Flt. Lt Asaniyi.

“Na ce‘ kar ka damu, za ka je ka dawo.’ Ka je Enugu, Owerri sannan ka dawo Abuja. Munyi kiran bidiyo kuma munyi magana mai tsayi sannan kawai kayi ta yi mun murmushi. Ashe ban sani ba wannan shine murmushinka na ƙarshe.

“Sako na gaba da na samu shi ne cewa za ka tafi Kaduna. Zuciyata ta tarwatse, na ji ƙamshin haɗari, na fara kiranka, ba ka ɗauka ba. Me yasa ba ka dauka ba? Me ya sa? Ina so na roke ka da kada ka je.

“Wadannan watanni ukun sun kasance mini aljannar duniya. Muna cin abinci tare a cikin kwano ɗaya, muna yin addu'a tare, muna dariya kuma muna kuka tare. Wannan ba shirin da ka yi min bane.

“Ka ce za ka kasance tare da ni a kodayaushe. Kamar mafarki ne cewa ba zan iya ganina ba. Na san za ka dawo wurina. Ba abin da nake gani sai sakonnin ta’aziyya. Ta yaya zan iya jure musu? Karanta su yana huda zuciyata.

“Ina jin kamar na gaza, na gaza dakatar da kai, na gaza dakatar da Asaniyi, wayyo Allahna, wayyo Allahna. Ka ga wannan."

Ga yadda ta wallafa a kasa:

Hakazalika, wata abokiyar marigayi Olufade, Esther David, a wata hira da jaridar The Punch, ta bayyana marigayin a matsayin mutum mai sanyin hali da saukin kai.

“Ya kasance abokina sosai. Mun kasance abokai na kut da kut. Har yanzu ina cikin damuwa; Ina fata dama mafarki ne. Na gaza yin bacci tun ranar Juma’a,” inji ta.

A gefe guda, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da babban jigon jam’iyyar APC na kasa, Bola Tinubu.

Sun yi ganawar ne kan rasuwar babban hafsan sojan kasa, Laftanar Janar Ibrahim Attahiru, da wasu hafsoshi goma.

Tinubu ya samu rakiyar Bisi Akande da wasu mambobin APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel