Da dumi-dumi: Tinubu da Akande sun ziyarci Buhari kan mutuwar Ibrahim Attahiru da sauransu

Da dumi-dumi: Tinubu da Akande sun ziyarci Buhari kan mutuwar Ibrahim Attahiru da sauransu

- Buhari ya gana da babban jigon jam’iyyar APC na kasa, Bola Tinubu

- Sun yi ganawar ne kan rasuwar babban hafsan sojan kasa, Laftanar Janar Ibrahim Attahiru, da wasu hafsoshi goma

- Tinubu ya samu rakiyar Bisi Akande da wasu mambobin APC

Yan kwanaki bayan rasuwar babban hafsan sojan kasa, Laftanar Janar Ibrahim Attahiru, da wasu hafsoshi goma, babban jigon jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, da shugaban rikon kwarya na jam'iyyar, Cif Bisi Akande, sun ya mika ta'aziyya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Hasali ma, Buhari ya ayyana Litinin, 24 ga Mayu, a matsayin ranar hutu ga mambobin rundunar Sojojin Najeriya don girmama mamacin.

KU KARANTA KUMA: APC ta yi babban rashi yayin da tsohon shugaban jam'iyyar da wasu mambobi 150 suka koma PDP a Abuja

Da dumi-dumi: Tinubu da Akande sun ziyarci Buhari kan mutuwar Ibrahim Attahiru da sauransu
Da dumi-dumi: Tinubu da Akande sun ziyarci Buhari kan mutuwar Ibrahim Attahiru da sauransu Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Buhari ya tarbe su a fadar shugaban kasa da ke Abuja, jaridar The Nation ta rahoto.

Asiwaju Tinubu da Cif Akande sun samu rakiyar wasu mambobin jam'iyyar a yayin ziyarar.

Hadimin shugaban kasa a shafukan zumuntar zamani, Bashir Ahmad ma ya tabbatar da ziyarar da shugabannin suka kai wa Buhari a shafinsa na Twitter.

KU KARANTA KUMA: Bakin ciki da tashin hankali a Benuwe yayin da Makiyaya suka kashe Manoma sama da 100 a garuruwa 4

Ya wallafa a shafin nasa:

"A daren jiya, Shugaba @Mbuhari ya samu ziyarar ta’aziyya daga shugabannin Kudu maso Yamma sakamakon mummunan hatsarin jirgin sama da ya faru a ranar Juma’a a Kaduna wanda ya yi sanadiyyar rasa rayukan marigayi Babban Hafsan Sojojin, Laftanar Janar Attahiru, tare da wasu hafsoshin soja 10."

A gefe guda, babban hafsan hafsoshin tsaro, Janar Lucky Irabor a ranar Litinin ya umarci sojoji da su daina jin zafi game da mutuwar Shugaban hafsan sojoji, Laftana-Janar Ibrahim Attahiru da wasu jami’ai 10 a wani hatsarin jirgin sama a Kaduna ranar Juma’a.

Da yake jawabi a gidan Attahiru da ke Abuja yayin addu’o’in kwana uku na Fidau, CDS ya bukaci sojojin su ci gaba da kasancewa masu kwarin gwiwa tare da mai da hankali kan matsayinsu na tsarin mulki, Daily Trust ta ruwaito.

“Sako na ga mambobin rundunar sojojin Najeriya shi ne cewa su ci gaba da jajircewa tare da kwazo kan matsayin su na tsarin mulki a wannan lokacin jarrabawa. Bai kamata karsashinsu yayi sanyi ba game da lamarin da ya faru,'' inji Irabor.

Asali: Legit.ng

Online view pixel