Bakin ciki da tashin hankali a Benuwe yayin da Makiyaya suka kashe Manoma sama da 100 a garuruwa 4
- Akalla manoma 100 ne wasu da ake zargin makiyaya ne dauke da makamai suka kashe a jihar Benuwe
- Alfred Atera, shugaban karamar hukumar Katsina-Ala ya tabbatar da mummunan ci gaba da kuma yawan mutanen da suka mutu
- Kashe-kashen da suka faru daga ranar Juma’a, 21 ga Mayu, zuwa Litinin, 24 ga Mayu, sun shafi Yooyo, Utange, Mbatura / Mberev, da Mbayongo
Wasu ‘yan bindiga da ake zargin makiyaya ne dauke da makamai sun kashe sama da mutane 100 a karamar hukumar Katsina-Ala da ke jihar Benuwe.
Jaridar The Guardian ta rahoto cewa kisan ya fara ne a daren Juma’a, 21 ga Mayu, har zuwa safiyar Litinin, 24 ga Mayu.
Shugaban karamar hukumar Katsina-Ala, Alfred Atera, ya tabbatar da adadin wadanda suka rasa rayukansu daga lamarin.
KU KARANTA KUMA: Ina kula da su kuma ina biya masu dukka bukatunsu: In ji matar da ta auri maza 7 a cikin wani bidiyo
Shugaban karamar hukumar ya koka kan yadda mutanensa ke neman mafaka domin tsira yayin da makiyayan ke harbi kan mai uwa da wabi kuma suka cika gawarwaki.
A cewar Atera, yankunan da harin ya shafa sun hada da, Yooyo, Utange, Mbatura/Mberev, da Mbayongo, jaridar ThisDay ta ruwaito.
An tattaro cewa makiyayan sun bankawa gidajen mutane wuta tare da lalata gonaki.
KU KARANTA KUMA: Magidanci ya tattara kayansa ya bar gida, ya ce matarsa na yawan dukansa, bidiyon ya haddasa cece-kuce
A wani labarin, jami'in gwamnatin jihar Ebonyi ya bayyana cewa sabbin jami'an tsaron yankin kudu-gabas 'Ebubeagu' sun cafke mutum 37 da ake zargi suna shirin kai hari ofishin yan sanda da INEC a jihar.
Kwamishinan tsaro, Stanley Okoro-Emegha, shine ya bayyana wa manema labarai haka a Abakalike ranar Litinin, kamar yadda Premium times ta ruwaito.
Yace an kama waɗanda ake zargin ne a garin Agubia, ƙaramar hukumar Ikwa ranar Lahadi.
Asali: Legit.ng