Magidanci ya tattara kayansa ya bar gida, ya ce matarsa na yawan dukansa, bidiyon ya haddasa cece-kuce

Magidanci ya tattara kayansa ya bar gida, ya ce matarsa na yawan dukansa, bidiyon ya haddasa cece-kuce

- Wani tsohon bidiyon dan Najeriya, Tunde, yana kukan cewa matarsa ta Burtaniya ta wulakanta shi kuma dole sai da ya tattara kayansa zuwa titi ya sake bayyana a yanar gizo

- Mutane da yawa wadanda watakila ba su kalli cikakken bidiyon labarin ba sun tausaya wa mutumin

- Wani bidiyon Youtube wanda aka ruwaito yana dauke da muryar matarsa ta farko ya bayyana yadda mutumin ya bar iyalinsa don komawa ga wata mace

Wani bidiyo na wani dan Najeriya da aka nuno yana korafi bayan 'matarsa farar fata' ta fatattake shi a Burtaniya ya yadu a shafin Twitter tare da martani masu tarin yawa.

A wani rubutu da aka yi a ranar Juma'a, 21 ga Mayu, wani shafin Twitter @Oluomoofderby wanda ya yada bidiyon ya yi masa lakabi da:

"Wasu mazan Najeriya na matukar shan wahala a Burtaniya."

KU KARANTA KUMA: Ina kula da su kuma ina baya masu dukka bukatunsu: In ji matar da ta auri maza 7 a cikin wani bidiyo

Magidanci ya tattara kayansa ya bar gida, ya ce matarsa na yawan dukansa
Magidanci ya tattara kayansa ya bar gida, ya ce matarsa na yawan dukansa Hoto: @Oluomoofderby
Asali: Twitter

A cikin faifan bidiyon, Tunde tare da jakunkunan kayansa a waje da kuma faffadan Talbijin ya yi magana mai daci kan yadda duk da biyan kudin jingina da kuma tsabtace gidan da yake yi, amma matar ta hana sa kwanciyar hankali.

Wani bincike da Legit.ng ta yi ya nuna cewa bidiyon ya fara shiga yanar gizo ne a shekarar 2020 kuma wani gidan YouTube da ake kira Obodo Oyinbo TV ne ya yada shi kuma yayi karin bayani game da lamarin.

A cikin bidiyon na YouTube, mai watsa shirin ya bayyana cewa mutumin dan Najeriya ya yi watsi da matarsa ta farko da yaransa ya koma ga farar fata saboda neman katinsa na dan kasa.

Kalli bidiyon a kasa:

Matar ta kara da cewa mutumin na girbe abunda ya shuka ne kuma bai taba kula da iyalinsa ba lokacin da yake 'da kudi'.

KU KARANTA KUMA: Gwamna Wike ya bugi kirji ya bayyana abunda zai faru da PDP idan ya fice

Ga bidiyon na Twitter a kasa:

Legit.ng ta tattaro wasu martani game da bidiyon mutumin da ya sake bayyana akan manhajar twitter:

@iamjoycelewis ya ce:

"Godiya ga Allah kan yanci da rayuwa. Ina addu'a ga maza da mata da ake cutarwa, da fatan Allah ya turo maka da taimako."

@adewale20280713 ya ce:

"Wasu 'yan Najeriya suna wahala a cikin kasar mu ma."

@ Utoks_4 ya ce:

"Kusan ban taɓa jin tausayin waɗannan mazajen ba. Yawancinsu suna yin ba daidai ba kuma suna barin ainihin matansu da iyalansu yawancin lokuta. Lool..abunda ya shuka wataƙila ??"

@achalaugom ta ce:

"Ina kallo kawai na san cewa akwai wata a kasa ... na so ace zan iya bayyana nawa halin da na shiga, da fatan wata rana zan sami karfin gwiwar yin hakan... wadannan mutanen na iya zama mummunan abu amma ƙarshe sai su ce su aka azabtar. Ta cika da shi!!! "

A wani labarin, Shehu Sani, ya yi sharhi kan kudurin majalisar wakilai na dakatar da yi wa kasa hidima a karkashin shirin NYSC da aka saba a Najeriya.

Rahoto ya bayyana cewa, majalisar wakilai ta yi zama na biyu kan yunkurin soke shirin bautar kasa a Najeriya kwata-kwata.

Shehu Sani, wanda yake tsohon sanata mai wakilatar Kaduna ta tsakiya, ya bayyana haka a daren Litinin 24 ga watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel