'Yan bindiga sun kai hari kan iyakar Neja da ke kusa da Abuja, sun sace mutum 12

'Yan bindiga sun kai hari kan iyakar Neja da ke kusa da Abuja, sun sace mutum 12

- An kai hari karamar hukumar Suleja ta jihar Neja a ranar Laraba, 19 ga Mayu

- Anyi garkuwa da mutane 12 a harin da aka gudanar da daddare

- Maharan sun kuma kashe wani mutum, wanda har yanzu ba a bayyana sunansa ba

'Yan bindiga dauke da makamai sun yi nasarar sace akalla mutane 12 mazauna garin Kwankwashe da ke karamar hukumar Suleja a jihar Neja yayin wani hari.

A cewar jaridar The Cable, maharan sun afkawa kauyen wanda ba shi da nisa da Abuja sannan suka kashe a kalla mutum daya.

An ce maharan sun mamaye kauyen tsawon sama da awa guda kafin jami’an ‘yan sanda suka shiga tsakani.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Nasarawa ta bai wa sarakunan gargajiya motoci sama da Naira miliyan 800

'Yan bindiga sun kai hari kan iyakar Neja da ke kusa da Abuja, sun sace mutum 12
'Yan bindiga sun kai hari kan iyakar Neja da ke kusa da Abuja, sun sace mutum 12 Hoto: @PremiumTimesng
Asali: UGC

Garin da aka kai harin yana misalin mintuna 30 zuwa Abuja, inda hukumomi suka kasance cikin shirin ko ta kwana bayan da 'yan ta'addan suka fatattaki wasu garuruwa a Neja.

Jaridar Premium Times ma ta ruwaito cewa wani mazaunin garin wanda ya bukaci a sakaya sunansa saboda dalilan tsaro, ya ce kimanin mutane 12 aka tabbatar da batar su yayin da aka kashe daya a wurin kafin su sace matar tasa.

KU KARANTA KUMA: Da duminsa: Abun fashewa ya sake tashi a Abeokuta, ya raunata 2 yan awanni bayan na dakin karatun Obasanjo

"Ina iya tabbatar muku da cewa 'yan bindigar sun kashe mutum daya, sun yanka masa wuya kafin su tafi da matarsa," majiyar ta shaida wa jaridar.

Wani mazaunin garin wanda kawai ya bayyana kansa a matsayin Kay, ya ce 'yan bindigar da suka far wa al'ummar ba su gaza 30 ba kuma suna sanye da kayan sojoji.

"Ban gan su ba yayin harin amma mutanen da suka gan su sun ce suna sanye da kayan sojoji," in ji Mista Kay.

A wani labarin, dan gidan Sarkin Kontagora, Alhaji Bashar Saidu Namaska, na cikin mutanen da yan bindiga suka hallaka yayinda suka kai hari gonar Sarkin a ranar Laraba, 19 ga Mayu, 2021.

Daily Trust ta ruwaito cewa 'dan Sarkin na tare da wasu mutane ne cikin gona dake titin Zuru lokacin da yan bindiga suka kai musu farmaki.

Yan bindigan sun yi awon gaba da shanu da dama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel