Gwamnatin Nasarawa ta bai wa sarakunan gargajiya motoci sama da Naira miliyan 800

Gwamnatin Nasarawa ta bai wa sarakunan gargajiya motoci sama da Naira miliyan 800

- Akalla sarakunan gargajiya 25 ne suka karbi sabbin motoci kirar SUV da darajarsu ta kai sama da Naira miliyan 800 a Nasarawa

- Gwamna Abdullahi Sule ya gabatar da motocin ga masarautun ne a yayin bikin cikarsa shekaru biyu a karagar mulki

- A cewar Sule, motocin za su saukakawa sarakunan sauke nauyin da ke kansu na masarautun

A ranar Talata 18 ga watan Mayu, Gwamna Abdullahi Sule ya gabatar wa sarakunan gargajiya 25 na ajin farko a jihar Nasarawa da sabbin motocin SUV.

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa idan har an sayi motocin ne kai tsaye daga kamfanin da ya kera su, za a kiyasta farashin su kan sama da Naira miliyan 800.

Sule ya gabatar da makullan sabbin Lexus 25 ga sarakunan a gidan gwamnati da ke Lafiya domin bikin cikarsa shekaru biyu akan karagar mulki.

KU KARANTA KUMA: Da duminsa: Abun fashewa ya sake tashi a Abeokuta, ya raunata 2 yan awanni bayan na dakin karatun Obasanjo

Gwamnatin Nasarawa ta bai wa sarakunan gargajiya motoci sama da Naira miliyan 800
Gwamnatin Nasarawa ta bai wa sarakunan gargajiya motoci sama da Naira miliyan 800 Hoto: @Opetuyii
Asali: Twitter

Gwamnan ya bayyana cewa an raba motocin ne domin saukaka hakkokin da ya rataya a sarakunan duba da mahimmiyar rawar da suke takawa wajen tabbatarwa da wadatar tsaro a jihar.

Yayin da gwamnatin jihar ta ce karamar hukumar ce ta fara wannan karimcin, amma sun yi shiru game da nawa aka kashe don sayen motocin da kuma tushen kudin.

Muazu Aminu, shugaban kungiyar kananan hukumomin Najeriya (ALGON) a Nasarawa ya ce masu ruwa da tsaki ne suka yi tunanin aikin, ciki har da shugabannin kananan hukumomi da kuma ma'aikatar ci gaban kananan hukumomi da harkokin sarakuna.

Aminu ya kuma bayyana cewa aikin ya samu amincewar gwamnatin jihar.

KU KARANTA KUMA: Jerin jiragen yaki masu karfi 26 da gwamnatin Buhari ta siya tun daga 2015

Wannan ci gaban na zuwa ne yayin da gwamnatin jihar ke rike da albashin ma'aikata na watanni biyu. Matakin ya jawo martanin 'yan Najeriya inda wasu ke bayyana shi a matsayin wani fifiko mara amfani.

Sai dai kuma, Sule yayin ayyuka don bikin cikarsa shekara biyu a kan mulki ya yi alkawarin biyan dukkanin albashin da ma’aikatan kananan hukumomi suke bi, Voice of Nigeria ta ruwaito.

Gwamnan wanda ya bayyana haka yayin da yake mika gaisuwa ga mai martaba Sarkin Nasarawa, Alhaji Ibrahim Jibril ya ce share albashin ma’aikata zai inganta yanayin rayuwa da inganta zaman lafiya a majalisu daban-daban.

A wani labarin, Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta yi babban kamu da mambobin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Ribas.

An tattaro cewa manyan jiga-jigan APC 11 ne suka sauya sheka zuwa jam'iyyar adawar cikin mako guda a jihar.

Hakan ya kasance ne sakamakon rikicin cikin gida da APC ke fama da shi a reshenta na Ribas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel