Da duminsa: Yan bindiga sun bindige 'dan Sarkin Kontagora har lahira

Da duminsa: Yan bindiga sun bindige 'dan Sarkin Kontagora har lahira

- Yan bindiga sun kai mumunan hari garin Kontagora dake jihar Neja

- Wannan ya biyo bayan kisan Sojoji uku da yan bindiga sukayi a jihar

- Yan bindiga sun yi awon gaba da wasu yayinda suka kwacewa sauran wayoyi da kudade

Dan gidan Sarkin Kontagora, Alhaji Bashar Saidu Namaska, na cikin mutanen da yan bindiga suka hallaka yayinda suka kai hari gonar Sarkin a ranar Laraba, 19 ga Mayu, 2021.

Daily Trust ta ruwaito cewa 'dan Sarkin na tare da wasu mutane ne cikin gona dake titin Zuru lokacin da yan bindiga suka kai musu farmaki.

Yan bindigan sun yi awon gaba da shanu da dama.

Majiyoyi sun bayyana cewa yan bindigan sun yi matafiya a hanyar fashi da makami inda suka kwace wayoyi, kudade da wasu kayayyaki hannunsu.

A cewar majiyoyin, an lallasa duk wanda bai da kudi ko dukiya kuma akayi awon gaba da su cikin daji.

'Dan sarkin wanda shine Sardaunan Kontagora ya kasance mai taya mahaifinsa Sarkin Sudan, Alhaji Saidu Namaska, abubuwa tunda ya fara rashin lafiya.

DUBA NAN: Bayan Komawa APC, Ayade Ya Aike Da Muhimmin Saƙo Ga Tsaffin Takwarorinsa a PDP

Da duminsa: Yan bindiga sun bindige 'dan Sarkin Kontagora har lahira
Da duminsa: Yan bindiga sun bindige 'dan Sarkin Kontagora har lahira
Asali: Original

KU KARANTA: Shugabannin PDP sun shiga ganawa kan sauya shekar gwamnan Kross Ribas

Wani ma'aikacin gwamnatin jihar wanda ya bukaci a sakaye sunansa ya bayyanawa Daily trust cewa da gaske ne.

"Da gaske ne yan bindiga sun kai hari garin Kontagora kuma sun harbi mutane sun kashe dan sarki Alhaji Bashar. Za'a sanar da mutuwar nan ba da dadewa ba kuma za'a birnesa," yace.

"An garzaya da shi asibiti bayan harbinsa amma an ce ya mutu."

A bangare guda, rundunar ‘yan sanda reshen jihar Imo ta tabbatar da cewa wasu 'yan bindiga cikin kakin soji sun kashe wani jami’inta, Sajan Loveday Obilonu, a hanyar Okwu Uratta da ke Owerri, jihar Imo, Vanguard ta ruwaito.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Abutu Yaro, ya bayyana hakan ga manema labarai a Owerri, ta bakin jami’in hulda da jama’a na yan sanda na jihar, Bala Elkana.

Abutu ya ce Sajan Loveday na daga cikin jami'an da aka tura don kare 'yan jihar daga masu aikata laifuka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng