Da duminsa: Abun fashewa ya sake tashi a Abeokuta, ya raunata 2 yan awanni bayan na dakin karatun Obasanjo

Da duminsa: Abun fashewa ya sake tashi a Abeokuta, ya raunata 2 yan awanni bayan na dakin karatun Obasanjo

- Abun fashewa ya sake tashi a Abeokuta yan awanni bayan na dakin karatun Obasanjo

- A wannan karon, lamarin ya faru ne harabar ginin CSCC, a yankin Onikoko na jihar Ogun

- Tukunyar gas da ke ajiye ce ta fashe lamarin da ya jikkata wasu mutane biyu

Kimanin awanni 24 bayan fashewar iskar gas ya faru a harabar dakin karatu na shugaban kasa Olusegun Obasanjo da ke Abeokuta, wani lamarin ya sake faruwa a harabar ginin CSCC, a yankin Onikoko na jihar.

Jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito cewa mutane biyu sun samu mummunan rauni a fashewar gas din kuma an garzaya dasu zuwa asibiti mafi kusa domin kula da lafiyarsu.

KU KARANTA KUMA: Jerin jiragen yaki masu karfi 26 da gwamnatin Buhari ta siya tun daga 2015

Da duminsa: Abun fashewa ya sake tashi a Abeokuta, ya raunata 2 yan awanni bayan na dakin karatun Obasanjo
Da duminsa: Abun fashewa ya sake tashi a Abeokuta, ya raunata 2 yan awanni bayan na dakin karatun Obasanjo Hoto: @dabiodunMFR
Asali: Twitter

Legit.ng ta tattaro cewa tukunyar gas da ke cike da gas ya fashe lokacin da ba a amfani da shi.

Sahara Reporters ta kuma ruwaito cewa fashewar tukunyar gas din ta shafi gine-gine da dama a kan hanyar Onikoko-Adigbe, motoci da wani malami a kwalejin St. Louis da ke Abeokuta.

Jaridar ta lura cewa, kwamishinan ayyuka na musamman na jihar, Femi Ogunbanwo, da sakataren dindindin a ma’aikatar, Kehinde Onasanya, da sauran jami’an jihar, sun kai ziyarar gani da ido wurin da abun ya faru.

A gefe guda, mun ji a baya cewa a kalla mutane biyu ne suka rasu sakamakon fashewar bututun iskar gas a cikin harabar Dakin Karatu na tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo Presidential Library (OOPL) da ke Abeokuta jihar Ogun a safiyar ranar Alhamis, rahoton Daily Trust.

KU KARANTA KUMA: Jerin sunayen shugabannin jam'iyyar APC da suka sauya sheka zuwa PDP a jihar Ribas a cikin mako guda

Dakin karatun ba shi da nisa da wani otel inda fashewar gas ya kashe mutane hudu kwanaki biyu da suka gabata.

Otel din mai suna Conference Hotel inda abin bakin cikin ya faru mallakin tsohon gwamnan jihar Ogun Gbenga Daniel ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel