Da Ɗuminsa: Abun Fashewa Ya Kashe Mutum 2 a Ɗakin Karatu Na Obasanjo Da Ke Abeokuta

Da Ɗuminsa: Abun Fashewa Ya Kashe Mutum 2 a Ɗakin Karatu Na Obasanjo Da Ke Abeokuta

- Mutane biyu sun riga mu gidan gaskiya sakamakon fashewar iskar gas a dakin karatun shugaban kasa Obasanjo da ke Ogun

- Rahotanni sun bayyana cewa makinai ne ke kokarin saka iskar gas a na'urar sanyaya daki, AC, kwatsam dai abin ya fashe

- Tuni dai jami'an hukumar kashe gobara na jihar sun isa wurin da abin ya faru domin bada gudunmawarsu wurin kashe wuta

A kalla mutane biyu ne suka rasu sakamakon fashewar bututun iskar gas a cikin harabar Dakin Karatu na tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo Presidential Library (OOPL) da ke Abeokuta jihar Ogun a safiyar ranar Alhamis, rahoton Daily Trust.

Dakin karatun ba shi da nisa da wani otel inda fashewar gas ya kashe mutane hudu kwanaki biyu da suka gabata.

Yanzu-Yanzu: Mutum Biyu Sun Mutu Bayan Fashewar Wani Abu a Obasanjo Library
Yanzu-Yanzu: Mutum Biyu Sun Mutu Bayan Fashewar Wani Abu a Obasanjo Library
Asali: Original

DUBA WANNAN: Allah Ya Yi Wa Sarkin Funakaye Muhammadu Kwairanga Abubakar II Rasuwa

Otel din mai suna Conference Hotel inda abin bakin cikin ya faru mallakin tsohon gwamnan jihar Ogun Gbenga Daniel ne.

Fashewar gas din a OOPL ya faru ne misalin karfe 11 na safe a wurin taro na Marque Event Centre da ke harabar dakin karatun na shugaban kasa.

Majiyar Legit.ng ta tattaro cewa makanikai suna zuba gas ne cikin na'urar sanyaya daki wato AC a lokacin da ya fashe.

"An tabbatar da rasuwar mutane biyu," ma'aikacin a OOPL ya shaidawa wakilin majiyar Legit.ng.

An rufe kofofi biyu da za su isar da mutum cikin OOPL a lokacin da wakilin Daily Trust ya isa wurin da abin ya faru.

KU KARANTA: Bayan Komawa APC, Ayade Ya Aike Da Muhimmin Saƙo Ga Tsaffin Takwarorinsa a PDP

Masu gadi a wurin suna hana mutane shiga, ma'aikatan hukumar kashe gobara na jihar ne kadai da wasu ma'aikata aka bari suka shiga.

A wani rahoton daban kun ji cewa abin baƙin ciki ya faru a unguwar Alanamu da ke ƙaramar hukumar Ilorin ta Yamma a ranar Talata a lokacin da wani mutum Alhaji Taiye-Hassan Beki ya rasa ransa sakamakon gini da ya faɗo masa.

Daily Trust ta ruwaito cewa marigayin, Injiniyar lantarki mai yara huɗu yana fitsari ne a bayan gidansa lokacin ana ruwan sama sai wani sashi na ginin ya faɗo masa.

An dauki lokaci kafin a kai masa ɗauki domin ƴan uwansa ba su san abin da ya faru da shi ba a lokacin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel