Gini Ya Faɗowa Wani Mutum Yayinda Ya Ke Fitsari a Bayan Gidansa

Gini Ya Faɗowa Wani Mutum Yayinda Ya Ke Fitsari a Bayan Gidansa

- Wani bawan Allah mai suna Alhaji Taiye-Hassan Beki mazaunin Ilorin ya mutu bayan gini ya faɗo masa

- Rahotanni sun nuna cewa Taiye-Hassan Beki ya fita bayan gidansa ya yi fitsari ne a lokacin ana ruwan sama sai gini ya faɗo masa

- Daga bisani da aka gano abin da ya faru da shi an ɗaga an ciro shi an garzaya da shi asibiti inda daga baya ya ce ga garin ku

Abin baƙin ciki ya faru a unguwar Alanamu da ke ƙaramar hukumar Ilorin ta Yamma a ranar Talata a lokacin da wani mutum Alhaji Taiye-Hassan Beki ya rasa ransa sakamakon gini da ya faɗo masa.

Daily Trust ta ruwaito cewa marigayin, Injiniyar lantarki mai yara huɗu yana fitsari ne a bayan gidansa lokacin ana ruwan sama sai wani sashi na ginin ya faɗo masa.

Gini Ya Faɗowa Wani Mutum Yayinda Ya Ke Fitsari a Bayan Gidansa
Gini Ya Faɗowa Wani Mutum Yayinda Ya Ke Fitsari a Bayan Gidansa. Hoto: @daily_trust
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Sarkin Kano Ya Tsallake Rijiya Da Baya Bayan Jirgin Sama Ya Kusa Hatsari

An dauki lokaci kafin a kai masa ɗauki domin ƴan uwansa ba su san abin da ya faru da shi ba a lokacin.

An garzaya da shi Asibitin Koyarwa ta Jami'ar Ilorin, UITH, bayan an ciro shi daga kasan ginin amma ya rasu lokacin da ake masa magani.

Tuni dai an yi masa jana'iza bisa koyarwar addinin musulunci.

KU KARANTA: Yajin Aikin Kaduna: 'Zo Ka Kama Ni Idan Zaka Iya,' Wabba Ya Faɗawa El-Rufai

Jagora a gidan Magaji Beki, Alhaji Yahaya Olowo-Beki yayin da ya ke magana kan lamarin ya ce ƙaddara ce daga Allah kuma ya yi addu'ar Allah ya bawa iyalansa haƙurin jure rashinsa.

A wani labarin daban, kun ji Hukumar Raya Birnin Tarayya Abuja, FCTA, ta rushe wani tashar tasi a NICON Junction, Maitama, Abuja, kan zargin mayar da tashar matattarar yan kwaya da bata gari, Daily Trust ta ruwaito.

Direktan (FCTA), sashin tsaro, Adamu Gwari, wanda ya yi magana yayin rushe tashar ya ce tashar barazanar tsaro ne sannan barazana ne ga muhallin mutanen da ke zaune a birnin. An Rushe Tashar Motar Saboda Ta Zama 'Matattarar Ƴan Ƙwaya' a Abuja.

Ya kuma ce rushe tashar mataki ne da aka dauka duba da irin kallubalen tsaron da ake fuskanta a jihar.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel