Bayan Komawa APC, Ayade Ya Aike Da Muhimmin Saƙo Ga Tsaffin Takwarorinsa a PDP
- Gwamnan Cross Rivers, Farfesa Ben Ayade da ya koma jam'iyyar APC ya shawarci tsaffin takwarorinsa na PDP su bi sahunsa
- Gwamna Ayade ya bayyana hakan ne a jawabin da ya yi a gidan gwamnati da ke Calabar bayan ganawa da shugabannin APC na jihar
- Ayade ya ce akwai bukatar gwamnonin jihohi su hada kai da gwamnatin tarayya domin ganin an gudu tare an tsira tare
Ben Ayade, gwamnan jihar Cross Rivers ya bukaci sauran gwamnoni a tsohuwar jam'iyyarsa ta Peoples Democratic Party, PDP, su dawo jam'iyyar All Progresives Congress, APC, Daily Trust ta ruwaito.
Legit.ng ta ruwaito yadda Ayade ya sauya sheka daga jam'iyyar na PDP ya koma jam'iyya mai mulkin kasa wato APC
DUBA WANNAN: Da Ɗuminsa: Ƴan Bindiga Sun Halaka Direba Sannan Suka Sace Fasinjoji 13 a Nasarawa
Gwamnan na Cross Rivers ya yi jawabi ne a gidan gwamnati da ke Calabar inda ya yi taro da shugabannin jam'iyyar APC.
Ya ce akwai bukatar gare shi da sauran gwamnoni su yi aiki kut-da-kut da Shugaba Muhammadu Buhari.
Ayade ya ce, "Akwai bukatar mu hada hannu da Shugaba Buhari a kokarinsa na inganta da habbaka lamuran kasar nan.
"Ina bukatar sauran gwamnoni su yi koyi da ni su fahimci dalili na na shiga APC. Ya kamata mu yi aiki tare da shugaban kasa domin cigaba da hadin kan Nigeria. Akwai bukatar dukkan mu mu zauna tare da Shugaban kasa a teburi daya mu ceci Nigeria.
KU KARANTA: Gwamnan PDP Ya Yi Rajista a Makarantar Ƙera Takalma a Jiharsa
"Don haka nauyi ya rataya a wuya na in dawo da jihar Cross Rivers zuwa tsakiya domin inganta jihar. Da haka ne na ke ayyana kai na a matsayin mamba da kuma jagora na APC a jihar Cross Rivers."
A wani rahoton daban kun ji cewa abin baƙin ciki ya faru a unguwar Alanamu da ke ƙaramar hukumar Ilorin ta Yamma a ranar Talata a lokacin da wani mutum Alhaji Taiye-Hassan Beki ya rasa ransa sakamakon gini da ya faɗo masa.
Daily Trust ta ruwaito cewa marigayin, Injiniyar lantarki mai yara huɗu yana fitsari ne a bayan gidansa lokacin ana ruwan sama sai wani sashi na ginin ya faɗo masa.
An dauki lokaci kafin a kai masa ɗauki domin ƴan uwansa ba su san abin da ya faru da shi ba a lokacin.
Asali: Legit.ng