Allah Ya Yi Wa Sarkin Funakaye Muhammadu Kwairanga Abubakar II Rasuwa

Allah Ya Yi Wa Sarkin Funakaye Muhammadu Kwairanga Abubakar II Rasuwa

- Mai Martaba Sarkin Funakaye Alhaji Muhammadu Kwairanga Abubakar II ya riga mu gidan gaskiya

- Marigayin Sarkin ya rasu ne a safiyar ranar Alhamis 20 ga watan Mayun 2021 yana da shekaru 68

- Za a yi jana'izar marigayin sarkin a yau Alhamis a fadan sarkin Bajoga da ke karamar hukumar Funakaye da karfe 2 na rana

Mai martaba sarkin Funakaye a jihar Gombe Alhaji Muhammadu Kwairanga Abubakar II ya riga mu gidan gaskiya.

Sarkin ya rasu ne a safiyar yau Alhamis a Bajoga kamar yadda BBC ta ruwaito. Ya rasu yana da shekaru 68 a duniya.

Allah ya yi wa sarkin Funakaye Muhammadu Kwairanga Abubakar II rasuwa
Allah ya yi wa sarkin Funakaye Muhammadu Kwairanga Abubakar II rasuwa. Hoto: @bbchausa
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Sarkin Musulmi Sa'ad Abubakar Ya Ce Ba Za Ayi Yaki Ba a Nigeria

Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya mika sakon ta'aziyarsa ga iyalan sarkin da al'ummar masarautar da ma kasa baki daya bisa wannan babban rashin.

Ya bayyana marigayin sarkin a matsayin jarumi wanda ya sadaukar da rayuwarsa don hidimtawa mutanensa, jiharsa da kasa baki daya. Ya kara da cewa ba za a taba manta irin bajintarsa ba da kima a idon mutanensa.

A watan Mayun shekarar 2010 ne aka nada marigayi Sarki Muhammadu Kwairanga Abubakar II kan mulki.

KU KARANTA: Za a Ware Wa Masu Addinan Gargajiya Ranar Hutu Tamkar Sallah da Kirsimeti a Legas

Kamar yadda sanarwar ta ce, za a yi jana'izar marigayin sarkin a yau Alhamis misalin karfe 2 na rana a fadar Sarkin Bajoga da ke karamar hukumar Funakaye a jihar Gombe.

Ba a sanar da abin da ya yi sanadin rasuwar marigayin sarkin ba.

A wani labarin daban, kun ji Hukumar Raya Birnin Tarayya Abuja, FCTA, ta rushe wani tashar tasi a NICON Junction, Maitama, Abuja, kan zargin mayar da tashar matattarar yan kwaya da bata gari, Daily Trust ta ruwaito.

Direktan (FCTA), sashin tsaro, Adamu Gwari, wanda ya yi magana yayin rushe tashar ya ce tashar barazanar tsaro ne sannan barazana ne ga muhallin mutanen da ke zaune a birnin. An Rushe Tashar Motar Saboda Ta Zama 'Matattarar Ƴan Ƙwaya' a Abuja.

Ya kuma ce rushe tashar mataki ne da aka dauka duba da irin kallubalen tsaron da ake fuskanta a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: