Masu Garkuwa Da Mutane Sun Sace Matafiya 18 a Jihar Zamfara

Masu Garkuwa Da Mutane Sun Sace Matafiya 18 a Jihar Zamfara

- Yan bindiga sun kai hari garin Dansadau da ke karamar hukumar Maru a jihar Zamfara sun sace kaya da dabbobi

- Wani mazaunin garin Dansadau ya ce tunda farko yan bindigan sun sace matafiya 18 da suka tashi zuwa Gusau

- Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, SP Mohammed Shehu ya ce bai da masaniya kan sace mutanen 18

Yan bindiga sun kai hari Dansadau, babban gari na biyu a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara inda suka sace kayan mutane da dabobinsu kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Wani mazaunin garin, Husaini Yanbiyu ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa yan bindigan masu yawa sun afka garin ne misalin karfe 4 na yamma suna dauke da muggan bindigu suna harbe-harbe.

Masu Garkuwa Da Mutane Sun Sace Matafiya 18 a Jihar Zamfara
Masu Garkuwa Da Mutane Sun Sace Matafiya 18 a Jihar Zamfara. Hoto: @Channelstv
Asali: Twitter

KU KARANTA: Gini Ya Faɗowa Wani Mutum Yayinda Ya Ke Fitsari a Bayan Gidansa

Yanbiyu ya ce, "Kowa a garin ya fara guje-guje domin kada yan bindigan da ke harbe-harbe su halaka shi.

"A halin yanzu da muke magana da kai, babu kowa a cikin garin. A halin yanzu kowa yana cikin gidansa domin babu jami'an tsaro."

Da aka masa tambaya kan cewa ko akwai wadanda aka kashe, Yanbiyu ya ce, "Ba zan iy sani ba har sai sun tafi mun fito daga inda muke boye."

A cewarsa, tunda farko a ranar yan bindigan sun sace mutane 18 da ke kan hanyarsu ta zuwa Gusau a cikin motar bas.

KU KARANTA: Dogo Gide Ya Kashe 12 Cikin Yaransa Kan Rikicin Rabon Kayan Sata a Niger

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, SP Mohammed Shehu ya ce, "Rundunar yan sanda ba ta da masaniya kan sace mutanen 18. A kan harin da aka kai garin Dansadau da aka ce yan bindiga sunyi, zan sake tuntubarka."

Bai bada wani sabon bayani ba a lokacin hada wannan rahoton.

A wani labarin daban, kun ji Hukumar Raya Birnin Tarayya Abuja, FCTA, ta rushe wani tashar tasi a NICON Junction, Maitama, Abuja, kan zargin mayar da tashar matattarar yan kwaya da bata gari, Daily Trust ta ruwaito.

Direktan (FCTA), sashin tsaro, Adamu Gwari, wanda ya yi magana yayin rushe tashar ya ce tashar barazanar tsaro ne sannan barazana ne ga muhallin mutanen da ke zaune a birnin. An Rushe Tashar Motar Saboda Ta Zama 'Matattarar Ƴan Ƙwaya' a Abuja.

Ya kuma ce rushe tashar mataki ne da aka dauka duba da irin kallubalen tsaron da ake fuskanta a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel