Dogo Gide Ya Kashe 12 Cikin Yaransa Kan Rikicin Rabon Kayan Sata a Niger

Dogo Gide Ya Kashe 12 Cikin Yaransa Kan Rikicin Rabon Kayan Sata a Niger

- Rikici ya barke tsakanin shugaban yan bindiga Dogogide da yaransa a Kusasu ta jihar Niger

- Dogogide ya zargi yaransa ne da karya dokokinsa da kuma sace wasu daga cikin kayayyakin da suke yin fashinsu daga wurin mutane

- Wannan zargin ne ya fusata wasu daga cikin yan bindigan suka yi yunkurin kashe Dogogide amma ya kashe 12 cikinsu wasu suka tsere

Wani abu mai kama da dirama ya faru a ranar Juma'a a garin Kusasu, karamar hukumar Shiroro ta jihar Niger a lokacin da yan bindiga suka yi musayar wuta da ta yi sanadin mutuwar 12 cikinsu wasu kuma suka jikkata.

Wasu daga dama cikinsu sun tsere sun bar sansanin su da ke Kusasu saboda rashin jituwar da ta shiga tsakaninsu kamar yadda The Punch ta ruwaito.

'Yan Bindiga 12 Sun Mutu Kan Rikicin Rabon Kayan Sata a Niger
'Yan Bindiga 12 Sun Mutu Kan Rikicin Rabon Kayan Sata a Niger. @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Gini Ya Faɗowa Wani Mutum Yayinda Ya Ke Fitsari a Bayan Gidansa

Rikicin ya barke ne tsakanin shugaban yan bindiga Dogogide da yaransa bayan ya yi zargin suna makale wasu daga cikin kudadensa idan sun kai hari.

Dogogide daya ne daga cikin shugabannin yan bindiga uku da suka yi kaurin suna a yankunan kananan hukumomin Shiroro a Niger da Birnin Gwari a jihar Kaduna.

An ce Dogogide ya zargi yaransa da karya dokokin ayyukansu ta hanyar kashe mazauna kauyukan barkatai da keta mutuncin matan aure hakan yasa ya kira taro.

Ya kwace makamai daga hannun yaransa a lokacin da ya ke kokawa kan saba dokoki yana barazanar zai kore su ya dauki sabbi saboda 'rashin biyayyansu'.

A cewar wata majiya kusa da garin, wannan abin da Dogogide ya yi bai yi wa yaran dadi ba hakan yasa suka yi musaya maganganu mai zafi.

Sakamakon hakan ne daya daga cikin yaran ya yi yunkurin kashe shi a yayin da ya bude masa wuta amma bai yi nasara ba.

KU KARANTA: Yajin Aikin Kaduna: 'Zo Ka Kama Ni Idan Zaka Iya,' Wabba Ya Faɗawa El-Rufai

Majiyar ta ce a lokacin ne Dogogide da wasu tsiraru da ke masa biyayya suka bude wuta suka kashe 12 cikin 'wadanda ke rikicin da shi' yayin da sauran suka tsere.

Wata majiya daga garin ta ce bayan harbe-harben, yan bindigan sun shigo garin sun sace mutum 10 don su taya su birne yan uwansu da aka kashe.

Amma sun sako mutanen bayan sun gama birne gawarwakin tare da gargadinsu kada su fada wa kowa.

A wani labarin daban, jami'an yan sanda sun halaka a kalla yan ta'addan Boko Haram takwas da suka yi yunkurin kai wa mazauna garin Maidguri, babban birnin jihar Borno hari a yammacin ranar Talata, PRNigeria ta ruwaito.

Legit.ng ta ruwaito cewa yan ta'addan sun shiga cikin garin da motocci masu bindiga da babura da dama a ranar Talata yayin da musulmi ke shirin yin bude bakin azumin Ramadan. 'Yan Sanda Sun Kashe 'Yan Boko Haram 8 Da Suka Kai Hari Maiduguri.

Wata majiyar sirri ta shaida wa PRNigeria cewa yan ta'addan suna cikin kona gidajen mutane ne a Jiddari Polo a yayin da yan sandan karkashin jagorancin CSP Mohammed Ibrahim suka iso unguwar da mota mai bindiga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel