An Rushe Tashar Mota Saboda Ta Zama 'Matattarar Ƴan Ƙwaya' a Abuja

An Rushe Tashar Mota Saboda Ta Zama 'Matattarar Ƴan Ƙwaya' a Abuja

- Hukumar Raya Birnin Tarayya, FCTA, ta rushe tashar yan tasi da ke NICON Junction da ke Maitama a Abuja

- MInistan babban birnin tarayya, Muhammad Musa Bello ne ya bada wannan umurnin ya kuma ce a shuka tsirai a wurin

- Ministan ya ce an dauki wannan matakin ne domin tashar ya zama matattarar bata gari da mashaya wadda hakan ke barazana ga tsaron yan unguwar

Hukumar Raya Birnin Tarayya Abuja, FCTA, ta rushe wani tashar tasi a NICON Junction, Maitama, Abuja, kan zargin mayar da tashar matattarar yan kwaya da bata gari, Daily Trust ta ruwaito.

Direktan (FCTA), sashin tsaro, Adamu Gwari, wanda ya yi magana yayin rushe tashar ya ce tashar barazanar tsaro ne sannan barazana ne ga muhallin mutanen da ke zaune a birnin.

An Rushe Tashar Motar Saboda Ta Zama 'Matattarar Ƴan Ƙwaya' a Abuja
An Rushe Tashar Motar Saboda Ta Zama 'Matattarar Ƴan Ƙwaya' a Abuja. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Sarkin Muri Ya Umurci Mutanen Masarautarsa Su Yi Fito-Na-Fito Da Ƴan Bindiga

Ya kuma ce rushe tashar mataki ne da aka dauka duba da irin kallubalen tsaron da ake fuskanta a jihar.

"A tsarin birnin nan, wannan wurin tashar tasi ne amma an mayar da shi wurin aikata laifi. Hakan yasa muka cire komai a wurin. Wannan wurin ya zama barazanar tsaro. Mazauna unguwar na ta nuna damuwarsu kan karuwar laifuka da ke da alaka da wurin," in ji shi.

Ikharo Attah, shugaban kwamitin tsaftace Abuja wanda ya yi magana kan batun ya ce ministan Abuja, Malam Muhammad Musa Bello ya damu bisa barazanar da bata garin ke yi wa mazauna unguwar.

KU KARANTA: Da Ɗuminsa: ICPC Ta Fara Farautar Sirikin Buhari Ruwa a Jallo

Ya ce ministan Abuja ne ya bada umurnin rushe wurin domin tashar ta zama barazana ga mazauna unguwar kuma ya umurci dukkan hukumomin da nauyin ya rataya a kansu su tabbatar tashar ba ta dawo wurin ba.

"Ministan ya kuma bada umurnin cewa mu shukka tsirai a wurin domin kara kawata birnin na Abuja," in ji Attah.

A wani labarin daban kun ji cewa gwamnatin jihar Kano a ranar Litinin ta tabbatar da cewa mutane shida sun mutu sakamakon wata bakuwar cuta a karamar hukumar Minjibir a jihar, Vangaurd ta ruwaito.

Kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dr Aminu Ibrahim-Tsanyawa wanda ya tabbatar da hakan ya ce wasu mutum 46 da suka kamu da cutar na jinya a asibiti.

Ibrahim-Tsanyawa ya ce cutar ta bulla ne a kauyen Gandun Koya da ranar 7 ga watan Mayu kuma ta yadu zuwa garuruwan da ke makwabtaka da ita.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel