Rashin Tsaro: IBB Ya Bayyana Abinda FG Zata Yi Ta Magance Matsalar Tsaro Cikin Sauƙi

Rashin Tsaro: IBB Ya Bayyana Abinda FG Zata Yi Ta Magance Matsalar Tsaro Cikin Sauƙi

- Tsohon shugaban ƙasa,Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) ya shawarci gwamnatin tarayya da ta samar da makaman zamani ga jami'an soji

- IBB yace yana da yaƙinin cewa matukar gwamnati ta amince ta sake zama domin yin sabon tunani kan rashin tsaro a ƙasar nan, to zata cimma nasara cikin ƙanƙanin lokaci

- Yace suna iya ƙoƙarinsu wajen taimakawa gwamnati da shawarwari wajen warware dukkan ƙalubalen tsaro a ƙasar nan

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, yayi kira ga gwamnatin yarayya ta horad da jami'an soji tare da wadata su da makamai na zamani domin magance matsalar tsaro.

KARANTA ANAN: Rahoto Na Musamman: Yadda Jami’an Kwastam Suka Buɗe Wuta Ranar Sallah, Mutum 6 Suka Mutu

IBB, wanda ya nuna matuƙar damuwarsa kan halin da ake ciki na rashin tsaro yace ya kasance yana taimakawa da bayar da shawarwari ga gwamnati ba tare da kowa ya sani ba, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

Yace ya zama wajibi ga kowane ɗan ƙasa ya nuna goyon bayansa ga gwamnati da jami'an tsaro domin su kawo ƙarshen matsalar tsaron da ake fama da shi.

Rashin Tsaro: IBB Ya Bayyana Abinda FG Zata Yi Ta Magance Matsalar Tsaro Cikin Sauƙi
Rashin Tsaro: IBB Ya Bayyana Abinda FG Zata Yi Ta Magance Matsalar Tsaro Cikin Sauƙi Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Yayin da aka tambayesa ko yana ganin waɗanda ke kan madafun iko suna wasa da lamarin kawo ƙarshen matsalar tsaro, IBB yace:

"Akwai abubuwa da yawa da yakamata su gyara, idan suka amince suka sake zama da tunani akan lamarin, ina da yaƙinin zasu samu nasara cikin sauki."

Yayin da yake jawabi a akan abinda ya kamata masu mulkin ƙasar nan a yanzun suyi, yace:

"Ku samar wa soji duk abinda suke buƙata, sannan ku tunasar dasu cewa wannan ƙasar su ce, kuma basu da wata ƙasa data fi ta."

"Sojin Najeriya na buƙatar makamai irin na zamani kuma suna buƙatar a horad da su. Ba wai kawai a siyo makamai a miƙa musu ba, ya zama wajibi a horad dasu yadda zasu yi amfani da makaman."

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Jami’an Tsaro Sun Harbe Yan Bindiga Huɗu Tare da Ma’aikaciyar Jinya

A ƙoƙarin da yake na taimakawa da shawarwari ga gwamnati domin ganin an kawo ƙarshen wannan matsala, wadda a yanzun take nema ta mamaye mahaifarsa, jihar Niger, IBB ya cigaba da cewa:

"Muna bada shawara dai-dai gwargwado, bamu yayata duk abinda muka faɗawa gwamnati. Ya zama wajibi mu haɗa kan mu, mu taimakawa waɗanda ke kan madafun iko, dukkan mu muna aiki ne don cimma kudiri ɗaya."

"Matsalar tsaro da rashin zaman lafiya, kowace gwamnati tana da nata ƙalubalen, ina tuna yadda muka yi yaƙi na tsawon shekara uku, a lokacin mutane sun taimaka wa gwamnati, gwamnati ta yi iya bakin ƙoƙarinta."

"Ba wai a Najeriya ne kaɗai ake samun irin wannan matsalar ba, kasashe da yawa sun shiga irin wannan, wasu saida suka ɗauki shekara 10 kafin su samu nasarar magance komai, ina da yaƙinin cewa watarana Najeriya zata fita daga cikin wannan ƙngin."

A wani labarin kuma Babu Makawa Sai Mun Hana Fulani Makiyaya Kiwo a Yankin Mu, Inji Gwamnan PDP

Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike , ya bayyana matsayar da ƙungiyar gwamnonin kudu suka yanke ta hana kiwo da ba gudu ba ja da baya.

Gwamnan ya jaddada cewa babu wnda zai sa gwamnonin su fasa zartar da hukuncin da gaba dayansu suka amince da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel