Babu Makawa Sai Mun Hana Fulani Makiyaya Kiwo a Yankin Mu, Inji Gwamnan PDP
- Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya bayyana matsayar da ƙungiyar gwamnonin kudu suka yanke ta hana kiwo da ba gudu ba ja da baya
- Gwamnan ya jaddada cewa babu wnda zai sa gwamnonin su fasa zartar da hukuncin da gaba dayansu suka amince da shi
- Ƙungiyar gwamnonin kudancin Najeriya sun nemi shugaba Buhari ya fito yayiwa yan Najeriya jawabi a kan halin da ake ciki
Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, yayi gargaɗin cewa matakin da gwamnonin kudancin ƙasar nan suka ɗauka na hana kiwo a yankin su, ba gudu ba ja da baya kuma ya kamata a girmama matakin.
KARANTA ANAN: Dubban Mutane Sun Yi Zanga-Zanga a Birnin Landan Kan Muzgunawa Falasdinawa
Gwamnan ya faɗi haka ne a wurin wata liyafa da aka shirya dominsa a Bori ƙaramar hukumar Khana ranar Asabar, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.
Yace ya kamata waɗanda ke sukar hukuncin da gwamnonin suka yanke a Asaba, Jihar Delta, su fahinci cewa babu wani ɓangare a ƙasar nan da yafi wani ɓangare.
Wike Yace: "Mun yanke hukunci kuma babu ja da baya, don haka masu kushe hukuncin mu ya isa haka. Mu ba na baya bane a cikin yan ƙasar nan, Muma mallakin ƙasar nan ne."
Gwamnonin kudu 17, karkashin Ƙungiyar gwamnonin kudancin ƙasar nan sun yake hukuncin cewa zasu hana kiwon shanu a faɗin yankin da suke jagoranta.
Gwamnonin sun yanke wannan matsayar ne a wajen taron da suka gudanar a gidan gwamnatin jihar Delta dake Asaba ranar Talatan da ta gabata.
KARANTA ANAN: Buhari ya yi magana da Shugaban Turkiyya game da muzgunuwar da Israila ta ke yi wa Falasdinawa
Ƙungiyar ta kuma yi kira ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta gudanar da sake fasalin ƙasar nan, sannan kuma yayi wa yan ƙasa jawabi a kan taɓarɓarewar tsaro.
Gwamnonin sun nuna matuƙar damuwar su ''a kan taɓarɓarewar tsaro a ƙasar nan, kuma sun roƙi shugaba Buhari da yayi wa yan ƙasa cikakken bayani ƙan halin da ake ciki, ko hakan zaisa yan Najeriya su samu ƙarfin guiwa"
A wani labarin kuma Masallatan da Aka sace Daga masallacin Katsina Sun Samu Yanci
Akalla mutane 11, ciki har da wani jariri, da aka sace daga masallacin Jibia da ke jihar Katsina ne suka sake samun ‘yanci.
An sace masu bautar ne a ranar Litinin a wani masallaci da ke bayan garin Jibiya na Jihar Katsina yayin da suke gudanar da sallar tahajjud.
Asali: Legit.ng