Da Ɗumi-Ɗumi: Jami’an Tsaro Sun Harbe Yan Bindiga Huɗu Tare da Ma’aikaciyar Jinya

Da Ɗumi-Ɗumi: Jami’an Tsaro Sun Harbe Yan Bindiga Huɗu Tare da Ma’aikaciyar Jinya

- Jami'an tsaro sun harbe wasu yan bindiga huɗu tare da wata ma'aikaciyar jinya dake kula da lafiyar su a jihar Lagos

- Ana zargin yan bindigan da aka ƙashe ɗin suna da hannu a hare-haren da aka kaiwa jami'an yan sanda a jihar makon da ya gabata

- Kwamishinan yan sandan jihar ya tabbatar da kashe yan bindigan amma yace ba hukumar yan sanda bace ta yi wannan aikin

An harbe wasu yan bindiga huɗu da suka tsere tare da ma'aikaciyar jinya ɗaya ranar Asabar a yankin karamar hukumar Oyigbo, jihar Rivers.

KARANTA ANAN: Kasar Afrika ta kudu na shirin kafa dokar halastawa mata auren namiji fiye da daya

Rahoton Dailytrust ya gano cewa yan bindigan suna daga cikin waɗanda suka kai hare-hare ga jami'an yan sanda a jihar makon da ya gabata, Inda jami'an yan sanda bakwai suka rasa rayukansu.

Kwamishinan yan sandan jihar Rivers, Sunday Eboka, ya bayyana cewa ba hukumar yan sanda ce ta jagoranci farmakin da aka kai har aka samu nasarar kashe waɗannan yan bindigan ba.

Da Ɗumi-Ɗumi: Jami’an Tsaro Sun Harbe Yan Bindiga Huɗu Tare da Ma’aikaciyar Jinya
Da Ɗumi-Ɗumi: Jami’an Tsaro Sun Harbe Yan Bindiga Huɗu Tare da Ma’aikaciyar Jinya Hoto: @dailytrust.com
Asali: UGC

Amma wata Majiya a yankin ta bayyana cewa wasu jami'an haɗin guiwa dake ƙoƙarin dawo da zaman lafiya a garin Oyigbo ne suka hallaka yan bindigan.

Majiyar tace ma'aikaciyar jinya mai suna Chichi na cikin duba lafiyar yan bindigan a wani kangon gini lokacin da jami'an haɗin guiwa suka iso wurin suk zagayesu sannan suka buɗe musu wuta.

KARANTA ANAN: Na Allah basu karewa: Dan sanda ya mayar da N1.2m da ya tsinta wurin hatsari a Kano

Majiyar tace: "A wancan lokacin da suka kaiwa yan sanda hari, jami'an yan sanda sun yi musayar wuta dasu, kuma da yawansu sun samu raunuka har suka manta da Motar Heliux da suka zo da ita."

"Waɗanda suka samu muggan raunukan sun gudu izuwa Maɓoyarsu, sanna suka nemi wata ma'aikaciyar jinya mai suna Chichi ta zo da yi musu magani."

"Jami'an tsaron ne suka gano maɓoyar su, a lokacin da suka isa wurin ana yiwa uku daga cikin su ƙarin ruwa. Ɗaya daga cikin yan bindigan yayi ƙoƙarin guduwa amma jami'an tsaron suka harbe shi.

"Jami'an tsaron sun shiga cikin kangon ginin inda suka haɗu da sauran ukun da akewa ƙarin ruwa tare da ma'aikaciya Chichi. Yan bindigan sun yi ƙoƙarin maida martanin harbi amma jami'an suka harbe su." a cewar majiyar.

Da aka tuntuɓi kwamishinan yan sanda na jihar, Friday Eboka, ya tabbatar da kashe yan bindigan amma yace ba hukumar yan sanda bace ta gudanar da aikin.

A wani labarin kuma 'Yan Najeriya ne ke ta rokona in fito takarar shugabancin kasa, Yahaya Bello

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello yace dukkan 'yan Najeriya ne ke ta rokonsa da ya fito takarar shugabancin kasa a 2023.

Gwamnan yace babu shakka akwai abinda mata da matasa suka hango a tare da shi ne, shiyasa suke ta wannan tururuwar garesa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel