Rahoto Na Musamman: Yadda Jami’an Kwastam Suka Buɗe Wuta Ranar Sallah, Mutum 6 Suka Mutu

Rahoto Na Musamman: Yadda Jami’an Kwastam Suka Buɗe Wuta Ranar Sallah, Mutum 6 Suka Mutu

- Mutum 6 ne suka rasa rayukansu a wata musayar wuta da aka yi tsakanin hukumar kwastam da yan fasa ƙwauri a ƙauyen Iseyin jihar Oyo

- Matasan garin sun harzuƙa da kisan da akayi wa mutane waɗanda babu ruwansu a rigimar, inda suka lalata wasu motocin jami'an kwastam

- Hukumar yan sanda tayi alƙawarin gudanar da bincike tun daga tushe, kuma tace zata yi adalci yayin aikinta

Ranar Alhamis 13 ga watan Mayu, ta kasance ranar murna da farin ciki ga musulmai a faɗin duniya kasancewarta ranar Sallar idi (Eidul Fitr) bayan kammala azumin watan Ramadana.

Amma hakan bata samu ba a ƙauyen Iseyin dake jihar Oyo, wanda keda nisan kilomita 74 daga Ibadan, babban birnin jihar.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Jami’an Tsaro Sun Harbe Yan Bindiga Huɗu Tare da Ma’aikaciyar Jinya

Rahoton Legit.ng ya gano yadda akayi musayar wuta tsakanin jami'an hukumar kwastam (NSC) da wasu yan fasa ƙwauri wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar mutum shida.

Rahoto Na Musamman: Yadda Jami’an Kwastam Suka Buɗe Wuta Ranar Sallah, Mutum 6 Suka Mutu
Rahoto Na Musamman: Yadda Jami’an Kwastam Suka Buɗe Wuta Ranar Sallah, Mutum 6 Suka Mutu Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Yan fasa ƙwaurin sun shiga musayar wuta da jami'an kwastam ɗin ne a ƙoƙarin su na ƙwace wata mota maƙare da buhunan shingafa da wasu kayayyaki daga hannun jami'an.

An tabbatar da mutuwar mutum shida bayan fafatawar tsakanin jami'an NCS da yan fasa ƙwaurin a Iseyin.

Amma da misalin ƙarfe 6:30 na yamma, an gano gawarwakin mazauna garin Iseyin guda shida a cikin ruwa biyo bayan harbi ba tare da la'akari ba da jami'an hukumar kwastam suka yi.

Shaidun gani da ido sun ce yan fasa ƙwaurin sun tafi ba tare da an cutar da su ba, yayin da jami'an kwastom suka ɗauki waɗanda suka ji rauni daga cikinsu suka yi gaba.

Wannan lamari ya jefa gaba ɗaya yan garin cikin ƙunci da baƙin ciki, wanda daga bisani ya tunzura matasa suka je suka ƙona motoci da gidajen da ake zargin na jami'an kwastam ne.

Meyasa a garin Iseyin?

Legit.ng ta binciko cewa a shekarar 2013, faɗa tsakanin kwastan da yan fasa ƙwauri yayi sanadiyyar mutuwar wani "Alhaji Were," ɗan siyasa kuma ɗan kasuwa.

Makamancin haka ya sake faruwa a lokacin Annobar COVID19 yayin da kwastan suka kai farmaki wani babban ɗakin ajiye kaya bayan sun sami rahoton an ajiye buhunan shinkafa.

Matasan yankin sun yi gaba-da-gaba da jami'an kwastan ɗin wanda hakan yakai ga harbe-harbe.

KARANTA ANAN: Babu Makawa Sai Mun Hana Fulani Makiyaya Kiwo a Yankin Mu, Inji Gwamnan PDP

Munyi harbin ne domin kare kanmu, inji kwastam

A wani jawabi da hukumar ta fitar ranar 14 ga watan Mayu ta hannun kakakin ta, DSC Theophilus P Duniya, domin maida martani kan lamarin da ya faru ranar 13 ga Mayu, NSC ta danganta harbin ga wasu sheɗanun yan fasa ƙwauri da suka shirya tare da taimakon wasu ɓarayi suka yi ƙoƙarin yin fasa ƙwaurin shinkafa yar ƙasar waje a garin Iseyin.

A wani ɓangare na jawabin, yace:

"A wani sintiri da jami'an mu suka fita sun kamo motocin Nissan Pathfinder SUV guda biyu maƙare da shinkafar fasa ƙwauri a garin Iseyin. Bayan wannan ne, Sai wasu mutane suka kaiwa jami'an hari waɗanda masu fasa ƙwaurin ne suka turo su."

"Mutanen ɗauke da manyan makamai sun farmaki jami'an NSC wanda hakan yayi sanadiyyar jami'ai biyu suka sami munanan raunuka."

Mazauna garin sun buƙaci ayi musu adalci

A wurin jin ta bakin jama'a wanda ya haɗa manyan mutane kamar; sarkin gargajiya na garin, Oba Salaudeen Adekunle Ologunebi. shugaban riƙon kwarya, Mufutau Abilawon, DPO na ofishin yan sandan yankin, Iyalan waɗanda aka kashe da ɗaruruwan matasa, waɗanda suka yi jawabi sun ce harbe-harben sun yi muni sabida waɗanda aka kashe mutane ne da babu ruwansu.

Rahoto Na Musamman: Yadda Jami’an Kwastam Suka Buɗe Wuta Ranar Sallah, Mutum 6 Suka Mutu
Rahoto Na Musamman: Yadda Jami’an Kwastam Suka Buɗe Wuta Ranar Sallah, Mutum 6 Suka Mutu Hoto: legit.ng
Asali: UGC

Yayin da yake jawabi a wajen taron wanda Legit.ng ta halarta, Chief Ismail Tikalosoro, yace sun gaji da halin jami'an kwastan a yankin.

"Bamu buƙatar jami'an kwastan a Iseyin" ya faɗa yayin da mutane suka yaba da maganarsa "abubuwan da suka mana ya ishe mu hakanan. Kashe mana mutane ya ishe mu hakanan."

Ya kuma yi kira da kowa ya kwantar da hankalinsa yayin da garin zai haɗa lauyoyinsa domin shigar da ƙarar hukumar kwastam.

Babu ruwansa meyasa aka kashe shi?

Yayin da yake zantawa da Legit.ng, daya daga cikin yan uwan wani da aka kashe, Timothy (Baba Joel), Wanda ya bayyana kansa da, Odunayo Kamaru, ya tabbatar da cewa wani harsashi ne yayi sanadiyyar mutuwar ɗan uwansa.

Yace: "Nayi matuƙar mamakin mutuwarsa, ɗan uwa na mutumin kirki ne wanda yake faɗi-tashi don cimma bukatunsa. Idan har baije wajen aikin Lebura ba, to zaka sameshi a gona, wani lokacin yana yin Okada idan bashi da kuɗi."

"Yana da mata da kuma 'ya'ya, har yanzun na kasa gane wane dalili ne yasa a kashe shi."

Zamu binciko tushen lamarin, hukumar yan sanda

Yayin da Legit.ng ta tuntuɓi ofishin kakakin hukumar yan sanda ta jihar Oyo, bata samu bayani ba, amma yayin da yayi jawabi a wajen taron ji daga bakin mutane, DPO na ofishin dake Iseyin yayi alƙawarin zasu gudanar da bincike akan lamarin.

Ya kuma yi alƙawarin za'a gudanar da adalci, ya kuma yi kira ga jama'a da su kwantar da hankalinsu don gujewa wata matsalar makamanciyar ta ENDSARS.

A wani.labarin kuma 'Yan Bindiga Sun Kwamushe Wani Babban Jami'in Kwastam, Sun Nemi Fansan N100m

Lamarin ya faru ne tsakanin karfe 1.00 na rana zuwa 2.00 na yamma, lokacin da wanda aka sacen da aka tura kwa nan nan zuwa yankin Ikom, ya dawo Calabar daga sansaninsa.

Ukweni, wanda aka ce dan kawu ne ga masanin dokoki, Mba Ukweni, Babban Lauyan Najeriya (SAN), zai yi ritaya nan ba da jimawa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel